Majalisar Wakilai tace za ta kawo gyara

Majalisar Wakilai tace za ta kawo gyara

– Shugaban majalisar dattawa za ta kawo gyara wajen sha’anin kasafin kudi

– Yakubu Dogara yace kasafin bana zai kawo karshen matasalar tattalin arziki

– Majalisar Dattawa na Kasar ta cire Sanata Ali Ndume daga matsayin sa jiya

Majalisar Wakilai tace za ta kawo gyara
Majalisar Wakilai tace za ta kawo gyara

Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara yace Majalisa za ta kawo gyara wajen sha’anin kasafin kudin Kasar. Dogara yace hakan zai kawo gaskiya tare da kuma rage kawo rikici da hayaniya kamar yadda aka samu wancan karo.

Shugaban Majalisar ya kuma bayyana cewa dole a maida hankali wajen kasafin kudin bana domin shi ne abu mafi muhimmanci a Kasar. Dogara yace kasafin kudin wannan shekarar, zai fitar da Najeriya daga kangin tattalin arziki.

KU KARANTA: An tsige Sanata Ndume

Dogara dai ya nemi Majalisar ta kara dagewa wajen aikin ta. Kakakin ya kuma tabbatar da cewa Majalisar sa za ta duba lamarin hana shigo da wasu kaya cikin Kasar da kuma karin haraji da Gwamnati tayi a wasu.

A jiya ne dai Shugaban Majalisa, Bukola Saraki ya karanta wata takarda daga ‘Yan APC mai nuna cewa sun cire Sanata Ndume daga matsayin sa. Sai dai Ndume yace wai don ya nemi Majalisa ta yi gaskiya wajen tantance Ibrahim Magu na EFCC shiyasa aka sauke sa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel