Wai! An sace gawa daga kabarinta a Afirka ta kudu

Wai! An sace gawa daga kabarinta a Afirka ta kudu

An nemi wasu gawawwaki guda biyu an rasa dake cikin kaburburansu a makabartan Nelspruit Qabrastan na kasar Afirka ta kudu.

Wai! An sace gawa daga kabarinta a Afirka ta kudu
Wai! An sace gawa daga kabarinta a Afirka ta kudu

Jaridar Daily Sun ta kasar Afirka ta kudu ta ruwaito wannan lamarin mai daure kai, inda tace an gani hakan ne bayan wasu gungun mutane mazauna yankin sun gano kaburbura guda biyu, amma ba gawa a cikinsu, sai dai kawai likkafanin mamatan aka tsinta.

KU KARANTA:An kaiwa sojojin Isra'ila mummunan hari

Masu lura da makabartan suna zargin a ranar Asabar 7 ga watan Janairu ne aka saci gawawwakin, wanda daya daga cikin su an birne tat un a 1960, dayar kuma a 2013.

Wani mazaunin unguwar Patricia Ngubane ya bayyana bacin ransa da faruwar lamarin, inda ya bukaci yansanda da suk tabbatar sun kama masu laifin. “abin da mamaki ace mutum zai je ya saci gawa, muna rokan yansanda dasu binciki lamarin” inji shi.

Suma masu musulman yankin Nelspruit sun yi alkawarin dauko hayan masu gadi a wani matakin magance sake faruwar lamarin.

Ku same a https://www.facebook.con/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel