LABARI DA DUMI-DUMI: Yan majalisar APC sun cire Ali Ndume a matsayin shugaba a majalisar dattawa

LABARI DA DUMI-DUMI: Yan majalisar APC sun cire Ali Ndume a matsayin shugaba a majalisar dattawa

An cire Sanata Ali Ndume na Kudancin Borno a matsayin jigon majalisar dattawa yayinda wasu alamu masu tsanani suka billo a ranar Talata, 10 ga watan Janairu, cewa rikicin cikin gida na jam’iyya mai ci ta All Progrssives Congress (APC) ya dauki wani sabon sauyi.

LABARI DA DUMI-DUMI: Yan majalisar APC sun cire Ali Ndume a matsayin shugaba a majalisar dattawa
Kusoshin APC sun cire Ali Ndume a matsayin shugaban majalisa sun mika sunan Sanata Ahmed Lawal a matsayin sabon shugaba

A wani sako da aka aika zuwa ga majalisar dattawa a ranar Talata, Kusoshin APC sun mika sunan Sanata Ahmed Lawal na Arewacin Yobe a matsayin sabon shugaba a majalisar dattawa.

A cewar kusoshin na jam’iyyar APC, an yanke hukuncin ne a lokacin taron kusoshin jam’iyya da akayi a ranar Litinin, 9 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Sama da mambobin APC 458 ne suka sauya sheka zauwa PDP a Plateau

A halin da ake ciki, Ali Ndume yayi watsi da cire shi da kusoshin APC sukayi a matsayin shugaba a majalisar dattawa.

“Har yanzu ni shugaba ne a majalisar dattawa,” Ndume yayi ikirin haka a lokacin taron manema labarai a majalisa a ranar Talata.

Ya kara da cewa shi baida masaniyan cire shi da kusoshin jam’iyyar APC sukayi.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel