Hotuna: hawaye na kwaranya kamar kogi yayinda yan Boko Haram suka kuma kashe wani jarumin Najeriya

Hotuna: hawaye na kwaranya kamar kogi yayinda yan Boko Haram suka kuma kashe wani jarumin Najeriya

Wani hoto ya kuma billowa yanar gizo, na wani jarumin soja wanda ya hadu da ajalinsa a hannun yan ta’addan Boko Haram.

Labari mara dadi da wani aboki

Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Ross Alabo-George ya buga dan takaitaccen labari kan mutuwar amininsa, kyaftin Victor Ulasi.

Ross ya bayyana abokinsa a matsayin mutun mara tsoro, wanda baza’a taba maida rashin sa ba.

Mummunan harin

Ross ya rubuta: “A yau, rahoton mutuwar abokina kuma abokin karatuna ya riske ni. Jiya, yan Boko Haram sun kai hari ga rundunan sojojin Najeriya 27 a Buni Yadi, karamar hukumar Gujba na jihar Yobe sun kuma kashe sojoji biyar."

Hotuna: hawaye na kwaranya kamar kogi yayinda yan Boko Haram suka kuma kashe wani jarumin Najeriya
Hotuna: hawaye na kwaranya kamar kogi yayinda yan Boko Haram suka kuma kashe wani jarumin Najeriya

Mutun mai tarin ilimi

Ya kasance dalibi mai kwazo a fannin kimiyya. Ya kammala karatunsa daga makarantar likitoci na Najeriya wato Medical College of the University of Nigeria kuma shine zakara a ajinsa.

Tambayan da na kasa ba kaina amsa

Har yanzu bazan iya bayanin dalilin da yasa ya shiga aikin soja ba. Ina tuna cewan na taba tambayar amininsa na makaranta Toni Ukachukwu “me Dr. Laco keyi a hukumar soji?” amma da nayi Magana dashi yan shekaru da suka wuce, na gane cewa. Yana so ya bauta wa Najeriya ne.

Hotuna: hawaye na kwaranya kamar kogi yayinda yan Boko Haram suka kuma kashe wani jarumin Najeriya
Hotuna: hawaye na kwaranya kamar kogi yayinda yan Boko Haram suka kuma kashe wani jarumin Najeriya

KU KARANTA KUMA: IBB na iya mutuwa a 2017, Bishop Emmah Isong yayi hasashe

Babu shakka, da ace bai shiga aikin soja ba, da yanzu ya zamo babban likita, kamar abokinmu Dr. Opara Augustine, babban likita, wanda ke zama kusa dani a aji. Amma ya zabi wannan kasar, ya kuma bauta mata tare da jaruman sojoji wanda ke yaki da karfinsu duk da halin da shugabancin kasar ke ciki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel