Buhari ya kori Sakataren Hukumar FRC

Buhari ya kori Sakataren Hukumar FRC

– Shugaban Kasa ya kori Shugaban Hukumar FRC ta Kasa

– An sallami Jim Obazee daga matsayin sa bayan wata ‘yar takaddama

– Buhari yayi sababbin nadi a Hukumar

Buhari ya kori Sakataren Hukumar FRC
Buhari ya kori Sakataren Hukumar FRC

Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Mista Jim Obazee daga matsayin sa na Shugaban Hukumar FRC ta Kasa. Ba tare da bata lokaci ba Shugaban Kasar ya nada Adedotun Sulaiman a matsayin wanda zai maye gurbin sa.

Garba Shehu ne dai ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar. Sulaiman ya rike Darekta da Kamfanin Arthur Anderson da kuma Accenture, kwarraren akawu ne wanda yayi karatu a Jami’ar Legas da Harvard ta Amurka.

KU KARANTA: ka ji abin da wani yayi wa tsohon Gwamna

An kuma umarni Ministan kasuwanci na Kasar ya nada sababbin masu kula da Hukumomin da ke karkashin Ma’aikatar. An dai samu matsala tsakanin Minista Enelemah da wanda aka sallama bayan ya dabbaka wata doka da ta nemi Shugabannin Addini su ajiye aiki bayan shekaru 20. Wannan dai ya kawo babban rikici musamman wajen Kirista.

Haka kuma, Mai magana da bakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu ya wanke Malam Abba Kyari daga zargi. Garba Shehu yace labarin da aka yada akan Malam Kyari karya ne, kazafi ne aka yi masa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel