An kama tsaffin jagororin 'yan tada kayar baya a shirye-shiryen ziyarar Osinbajo jihar Delta

An kama tsaffin jagororin 'yan tada kayar baya a shirye-shiryen ziyarar Osinbajo jihar Delta

-Sojoji sun kama tsaffin jagororin 'yan tada kayar baya a jihar Delta

An yi kamun ne a shirye-shiryen ziyarar da farfesa Yemi Osinbajo zai kawo jihar

-Mataimakin shugaban kasa zai kai ziyara Warri ranar Talata 10 ga watan Janairu

- Matasan kabilar Ijaw sun yi zanga-zanga inda su ka bukaci a yi gaggawar sakin tsaffin jagororin

An kama tsaffin jagororin 'yan tada kayar baya a shirye-shiryen ziyarar Osinbajo jihar Delta
An kama tsaffin jagororin 'yan tada kayar baya a shirye-shiryen ziyarar Osinbajo jihar Delta

An samu tashin hankali a yankin Niger-Delta ranar Lahadi 8 ga watan Janairu, biyo bayan kama wasu tsaffin jagororin 'yan tada kayar baya sanadiyyar ziyarar da mataimakin shugaban kasa zai kai masarautar Gbaramatu a karamar hukumar Warri maso Yamma ta jihar Delta ranar Talata 10 ga watan Janairu.

A cewar jaridar The Punch, sojoji sun mamaye gidajen tsaffin shuwagabannin 'yan tada kayar bayan su ka yi awan gaba da su.

An rawaito cewa, an kama wasu tsaffin 'yan tawaye da su ka hada da babban jagoransu mista Bounanawei Smith wanda a ka fi sani da sarkin daji, a wani tsattsauran matakin yaki da ta'addanci wanda a ka ce ba zai rasa nasaba da barazanar da tsagerun Niger-Delta ke yi ta kai hari a kan ma'aikatun mai ba.

An shirya Osinbajo zai kai ziyara masarautar Gbaramatu inda a ka haifi tsohon jagoran 'yan tawayen, Cif Ekpemupolo wanda a ka fi sani da Tompolo.

Makasudin ziyarar ta Osinbajo shi ne tattaunawa da shuwagabannin Gbaramatu wanda ya zama babbar cibiyar ayyukan 'yan tada kayar baya.

An dai tsaurara matakan tsaro a bangarorin garin da su ka hada da teku da kuma tudu. Yayin da a ka ajiye sojoji ruwa da kuma jiragen ruwan yaki a wurare daban-daban, sa'ilin da a ranar Lahadi da Asabar a ka ga motocin sojoji na sintiri a wuraren da a ke fargabar tashin tashina a jihar.

Majiyar da ke kusa da Smith ta fadawa manema labarai ranar Lahadi cewa, rundunar hadin gwiwa da a ka yi wa lakabi da: 'Operation Delta Safe' ta mamaye gidan tsohon shugaban 'yan tada kayar bayan a rukunin gidaje na Esiso da ke kan hanyar Eeffurun/Sapele a karamar hukumar Uvwie.

An ce tsohon jagoran ya na cikin ganawa da wasu 'ya'yan kungiyar Matasan Ijaw yayin da a ka yi zargin sojojin sun kutsa kai cikin gidan nasa kafin daga bisani su kama shi tare da wasu mutum 7 wadanda har lokacin da a ke hada wannan rahoton ba san ko su waye ba.

An kuma gano cewa sojojin sun kuma kama karin wasu tsaffin 'yan tada kayar bayan a ranar Asabar inda a ke tsare da su a sansanin sojin ruwa na Warri kafin a wuce da su hedikwatar tsaro ta Abuja.

Kwanannan dai gwamna Ifeanyi Okowa ya nada Smith mamba a kwamitin kula da tsaron hanyoyin kasa da na ruwa wadanda su ke aiki da jami'an tsaro don tabbatar da tsaro a jihar.

Yayin da a ke tambayar sa, kwamandan sojin ruwa NNS na jihar Delta Joseph Dzunve, ya tabbatar da cewa an kama mutane da dama kuma a na tsare da su a sansanin sojin ruwa da ke Warri. Amma ya ki yin cikakken bayani game da kamen.

Haka kuma mai magana da yawun kungiyar matasan Ijawa (IYC), Eric Omare ya tabbatar da kama tsaffin 'yan tada kayar bayan a wata sanarwa da ya fitar a Warri ranar Lahadi. Sanarwa da a ka bawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ta ce kungiyar matasan Ijaw ta ce gwamnatin tarayya ta na rura wutar tashin hankali a yankin Niger-Delta ta hanyara ci gaba da kamawa da tsare 'yan Niger-Delta musamman ma tsaffin jagororin 'yan tada kayar baya ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Kamen kwana kwanannan shi ne wanda a ka yi wa Bounanawei Smith wanda a ka fi sani da Sarkin Daji.

"Sojoji sun kama mista Bounanawei a gidan saukar bakinsa yayin da ya ke karbar bakuncin wasu mambobin Kungiyar Matasan Ijaw. Su ka mamaye su ka kuma binciki gidan bakin sama da kasa. Sannan wasu mambobin kungiyar ta IYC da su ke tare da shi sun sha da kyar yayin da sojojin su ka yi ta harbe-harben bindiga a gidan.

"IYC ta yi Allah wadai da wannan al'amarin. An sani cewa tun da a ka yafewa Bounanawei ya ke bada gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a yankin Niger-Delta musamman a jihar Delta."

IYC ta ce irin wannan mamaya da kamawa da kuma tsare 'yan Niger-Delta da sojoji ke yi ya zama ruwan dare a yankin.

Yayin da duniya ke bukukuwan sabuwar shekara a ranar 1ga watan Janairu 2017, su kuwa sojoji sun mamaye al'ummar Gbarun a karamar hukumar Kudancin Ijaw da ke jihar Bayelsa, su na harbi su ka kuma kama wani jagoran matasa, Kalmi Inakemenduo da sunan cewa shi dan tada kayar baya ne kuma har yanzunnan su na tsare da shi.

"Wannan kari ne a kan wasu matasan Ijaw ma su yawa da ke tsare irin su Aboy Muturu da Ezekiel Daniel da Victor Odogu (mai magana da yawun IYC na reshen Abuja) da kuma wasu da dama. Wadannan mutane sun kasance a hannun hukumar tsaro ta farin kaya da sojoji tun kimanin fiye da wata uku ba tare da an kai su kotu ba sannan ba a bada dalilin kama su ba." Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"A saki duk tsaffin 'yan tada kayar baya da jami'an tsaro su ka kama wadanda su ka hada da Smith da Aboy Muturu da Ezekiel Daniel da Victor Odogu da Kalami Inakemenduo da kuma sauran mutanen Ijaw da su ke tsare a wannan kasa nan take."

Ku biyomu a shafimnu na Facebook a https://www.facebook.com/naijcomhausa/ ko a Tuwita a https:twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel