Dangantakar Buhari da sabon Shugaban Kasar Ghana

Dangantakar Buhari da sabon Shugaban Kasar Ghana

– An rantsar da Nana Akufo-Addo a matsayin sabon shugaban kasar Ghana shekaran jiya

– Kamar Buhari, Nana ya doke Shugaba John Mahama daga kujerar sa bayan ya dade yana neman takara

– Shin wai wanene ma Nana Akufo-Addo? Ina kuma kamancecinyar Mulkin sa da Buhari?

Dangantakar Buhari da sabon Shugaban Kasar Ghana
Dangantakar Buhari da sabon Shugaban Kasar Ghana

An rantsar da Nana Akufo-Addo a matsayin sabon shugaban Kasar Ghana a karshen wannan makon. Nana Akufo-Addo ya doke shugaban kasa John Dramani Mahama daga kan kujerar sa a zaben da aka gudanar a watan Disamban bara kamar dai yadda Shugaba Buhari yayi da Jonathan Goodluck. Shugaba Buhari kuma ya kifar da Shagari ne a watan Disamban 1983.

Kamar yadda muka kawo an dai haifi Nana Akufo-Addo a tsakiyar Garin Accra, shekaru 72 da suka wuce. Watau dai kamar Shugaba Buhari na Najeriya, ya karbi mulki yana shekaru fiye da 70. Mahaifin sa, Edward Akufo-Addo yana cikin Alkalan farko na Kasar ya kuma rike shugabancin Kasar daga shekarar 1969 zuwa 1972. Sai dai shi Buhari ne ya rike Shugabanci a baya ba uban sa ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya mika ta'aziya ga mutanen Neja

Nana dai yayi karatu a Gida da kuma Kasar Ingila. Haka ma kuwa Shugaba Buhari na Najeriya ya leka Kasashe irin su Amurka inda yayi kwas din Soji. A shekarar 1975 Nana ya shiga aikin Kotu bayan ya karanci Ilmin tattali da kuma shari’a a Ingila. Yayi aiki a wurare da dama har da Amurka.

Akwai ma dai lokacin da ya rike Ministan shari’a na Kasar Ghana. Addo dai tun yana shekara 30 a Duniya yake siyasa. Haka Shugaba Buhari ya rike Gwamna da ma Minista, kuma tun yana matashi ya sha kifar da Gwamnati.

Nana Addo dai ya dade yana neman takarar shugabancin Kasar tun a shekarar 1998. Sai dai wannan karo ya samu. Haka a Najeriya Shugaba Buhari ya gwabza sau da dama kafin Allah yayi. Duk sun sha bugewa a Kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel