Rundunar Sojin Kasa za su saka wando daya da ‘Yan Neja-Delta

Rundunar Sojin Kasa za su saka wando daya da ‘Yan Neja-Delta

– Tsagerun Yankin Neja-Delta sun yi barazanar cigaba da barna a Yankin

– Rundunar Sojin Najeriya tace da su ‘kul’

– Sojoji sun sha alwashin kare Najeriya

Rundunar Sojin Kasa za su saka wando daya da ‘Yan Neja-Delta
Rundunar Sojin Kasa za su saka wando daya da ‘Yan Neja-Delta

Rundunar Sojojin Najeriya sun gargadi Tsagerun Neja-Delta da su guji tada zauna tsaye a Yankin Kasar mai arzikin mai. Sojojin sun yi alkawarin kare Kasar da kuma maganin duk wani Tsagera.

Kwanan ne dai Tsagerun Neja-Delta Avengers suka kira Mutanen su da su shiryawa yaki da gwamnatin tarayya domin kuwa ba a shiryawa lalama ba. Tsagerun sun ce ta tabbata Gwamnatin Buhari tana da taurin kai don haka ba ta jin komai sai an bullo ta wata hanyar dabam.

KU KARANTA: Janar IBB ya kusa mutuwa

Rundunar Sojin Kasar dai ta bakin Birgediya-Janar Rabe Abubakar wanda shine Darektan yada labarai yace Sojoji za su kare martabar Kasar da kare Jama’a daga ta’asar Tsagerun na Neja-Delta.

Sojojin Kasar dai sun ce ba su zura ido su kyale Tsagera sun rika barna a ko ina cikin Kasar ba. Rundunar ta kuma yi kira ga ‘Yan Kasa su zama masu kokari da kuma bada bayanai game da irin shirin wannan barna a fadin Kasar. Kwanaki dai har an janye wuta aka shiga ganawa domin sulhu tsakanin Tsagerun da Gwamnati, sai dai da alamu hakar sulhun ba ta fa ci ma ruwa ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel