Tsananin sanyi ya kashe mutum 20

Tsananin sanyi ya kashe mutum 20

- Wani muku-mukun sanyi da aka kwashe kwana da kwanaki ana yi ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 20 cikin kwana biyu a Turai

- Akasarin mutanen da suka mutu 'yan gudun hijira ne da kuma mutanen da ke kwana a waje

Tsananin sanyi ya kashe mutum 20
Tsananin sanyi ya kashe mutum 20

A ranar Asabar wasu yankunan kasar Rasha sun yi bukukuwan Kirsimeti ta mazahabin Orthodox cikin sanyin da ba a taba yin irin sa ba cikin sama da shekara 120.

Ma'aunin sanyi ya nuna cewa birnin Moscow yana shiga hali irin na wanda jaura ta wuce a kansa a dukkan dare.

Goma daga cikin mutanen da suka mutu a kasar Poland suke.

Haka kuma mutum bakwai ne suka mutu a Italiya, yayin da dusar kankara ta rufe kudu maso gabashi da kuma tsakiyar kasar.

Sauran mutum ukun sun mutu ne a Prague, babban birnin Jamhuriyar Czech, wanda ya fuskanci yanayin sanyin da bai taba fuskanta ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel