Yana ta sharbar kuka da neman gafara wurin Sule Lamido don ya zabi APC (Karanta)

Yana ta sharbar kuka da neman gafara wurin Sule Lamido don ya zabi APC (Karanta)

Wani bawan Allah kenan yake gursheken kuka a gaban tsohon gwamnan jihar jigawa Alh.Sule Lamido wai saboda kuskuren da yayi na zabar jam'iyyar APC a zabukan 2015.

Yana ta sharbar kuka da neman gafara wurin Sule Lamido don ya zabi APC (Karanta)
Yana ta sharbar kuka da neman gafara wurin Sule Lamido don ya zabi APC (Karanta)

Abin tambayar anan shine:

Anya kuwa kukan can na gaske ne ya kai har zuciya,

Ko kuwa wani sabon salo ne na maula da neman gindin zama?

A wani labarin kuma, A karshen satin da ya gabata ne dai ayarin jami'an 'yansandan jihar Jigawa suka shinga shingaye a kan hanyar shiga kauyen Bamaina mahaifar Sule Lamido tsohon gwamnan jihar ta Jigawa.

'Yan jam'iyyar PDP da 'yansandan jihar Jigawa suka kama sun je garin Bamaina ne domin ganawa da Sule Lamido tsohon gwamnan jihar, kuma jigo a jam'iyyar.

Amma acewar ASP Abdul Jinjiri kakakin rundunar 'yansandan jhar yace sun dauki matakin maka mutanen ne biyo bayan samun rahotannin siri dake cewa suna dauke da makamai.

Jinjiri yace lallai sun kama mutanen da makamai kuma makaman suna hannunsu da matasan da suka kama su dari da arba'in da takwas. Kawo yanzu ma tuni aka tasa keyarsu zuwa kotu.

Biyo bayan kama matasan majiyar mu ta nemi jin ta bakin shi Alhaji Sule Lamido akan lamarin. Yace wajen wata shida baya duk sati akalla mutane cikin motoci hamsin ko fiye zasu zo wurinsa. Yace za'a hana zumunci ne. Injishi kodayaushe yana zuwa ta'aziya da bikin daurin aure. Yace idan mutane sun taso daga Sokoto ko Enugu cikin motoci hamsin ko fiye sai ya gayawa 'yansanda su bashi izini domin za'a zo a gaisheshi?

Ya kira masu mulki su yi mulki masu hamayya kuma a barsu su cigaba da hamayya. Wannan ita ce siyasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel