Ma'aikatan gwamnati sun samu sabani kan ritayan Adeboye

Ma'aikatan gwamnati sun samu sabani kan ritayan Adeboye

Ma'aikatan gwamnati sun samu sabani kan ritayan Fasto EA Adeboye

Ma'aikatan gwamnati sun samu sabani kan ritayan Adeboye
Ma'aikatan gwamnati sun samu sabani kan ritayan Adeboye

Jaridar yau Litinin, 9 ga watan Disamba, ya bada rahoton rikici tsakanin ministan masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Mr. Okechukwu Enelamah, da sakataren ma'aikatar kula da harkokin kudaden wato Financial Regulatory Council of Nigeria (FRCN) Mr. Jim Obazee, akan wata sabuwar dika mai bada wa'adin shekara 20 ga shugabannin kungiyoyin addini ,fafutuka na kasa.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kashe soji 5

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa sabanin ya faru ne yayinda ministan ya aika wasika ga shugaban FRSC na umurtansa ya dakatad da wannan doka. Amma Obazee yayi kunnen kashi inda yace ministan bai da hurumin bashi irin wannan umurni tunda babu wani jawabin da yace a canza dokan ko kuma a dakatad dashi.

Ma'aikatar FRCN ,ta tabbatar da wannan sabani tsakanin ma'aikatun gwamnatin 2.

Majiyar tace wanda ministan masana'antu, kasuwanci da hannun jari, ya rubuta sako garemu cewa baya son a fara kaddamar da dokar saboda haka a dakatad da shi yanzu.

“Amma kun san a gwamnati, idan zaka dakatad da abu, sai ka kawo hujja. Har yanzu dai basu kawo hujja ba.”

https://www.facebook.com/naijcomhausa

https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel