Na haifan ma yan Boko Haram daban-daban 3 yara 3 – Amina

Na haifan ma yan Boko Haram daban-daban 3 yara 3 – Amina

Wata yar shekarar 15 Amina, wacce ta tsira daga hannun yan Boko Haram bayan shekaru 5 ta bayyana abinda ya far da ita.

Na haifan ma yan Boko Haram daban-daban 3 yara 3 – Amina
Na haifan ma yan Boko Haram daban-daban 3 yara 3 – Amina

Amina wacce ke da shekaru 20 yanzu ta fadawa jaridar The Mirror cewa mutuwan jaririnta wanda ya mutu a dajin Sambisa yayi masifar azabtar da ita.

“Na kasa kuka yayinda nake ganin jaririna za’a barshi cikin daji.”

Abin ya bata mata rai, Amina tace ba zata koma wajen yan Boko Haram din da suka kamata ba; tunda bata san inda zasuje ba.

KU KARANTA: Tsohon gwamnan jihar Neja ya kwanta dama

Tace: "Na barshi karashin bishiya, ina sa ran cewa wani abu zai kare shi. Kila gawanshi na nan har yanzu. Sun tilasta mini aure sau uku, kuma na Haifa ma kowanne cikinsu da."

Amina ta bayyana cewa ta kaiwa yayarta ziyara ne a garin Baba inda wata mota ta tsaya kawai suka dauke ta.

Da taki yarda sukayi mata dukan tsiya, bude idonta ke da wuya,sai taga kanta a dajin Sambisa, ta ga kanta cikin mata 200.

Game da cewarta,daya daga cikin yan matan na cikin yan makarantan Chibok saboda sun zama abokai, kuma har yanzu tana wajen.

Tace: “Ita an aura mata wani kuma ta haihu. Bata jin dadi, mijinta na da mata biyu kuma suna hanata abinci kana kuma yana dukanta."

https://www.facebook.com/naijcomhausa

https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel