Rayuka sun halaka yayinda Boko Haram suka kai hari Damaturu, ana tsoron sun koma Kaduna

Rayuka sun halaka yayinda Boko Haram suka kai hari Damaturu, ana tsoron sun koma Kaduna

- Anyi asaran rayuka yayinda aka kai hari Boko Haram jihar Yobe

- Rundunar soji ta ce mutane 5 aka rasa amma majiyoyi sun musanta hakan

- Akwai tsoron cewa yan Boko Haram sun fara komawa kudancin Kaduna

Rayuka sun halaka yayinda Boko Haram suka kai hari Damaturu,ana tsoron sun koma Kaduna
Rayuka sun halaka yayinda Boko Haram suka kai hari Damaturu,ana tsoron sun koma Kaduna

Game da cewar jaridan Punch, har yanzu ba’a san yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba, duk da cewa an tabbatar da cewa an kashe sojoj bayan harin da yan ta’addan suka kai barikin soji a Buni Yadi ranan asabar,7 ga watan Junairu.

Rahotanni sun nuna cewa harin da aka kaiwa soji 27 Brigade,ya faru ne misalin karfe 6 na yamma inda akayi mugun musayan wuta.

KU KARANTA: Kwanaki 1000 cir da sace yan matan Chibok

An tattaro cewa yan Boko Haram da dama sun halaka a artabun,kuma sauran sun gudu daji.

Duk da cewa kakakin rundunar 27 Brigade, Lt. George Okupe, yace rundunar sojin sun fitittiki yan Boko Haram din, bai tabbatar da yawan sojin da suka raa rayukansu ba.

Yace: “An kawo hari Buni Yadi mislain karfe 6 na yamma. Abubuwa na karkashin kulan mu. Har yanzu ba’a san yawan yan ta’adda da sojin da suka mutu ba. Amma zai bada cikakken bayani nan gaba.”

A bangare guda, wata majiyan soji yace wani likitan soji,da wasu soji 4 ne suka rasa rayuansu .

https://www.facebook.com/naijcomhausa

https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel