Boko Haram ta shiga uku, Najeriya ta sayi sabbin jiragen yaki daga Rasha

Boko Haram ta shiga uku, Najeriya ta sayi sabbin jiragen yaki daga Rasha

- Rundunar Sojin sama sun sayi Jirage mai saukar angulu Mi-35M guda 2

- Mugun jirage masu saukar angulu wacce take aiki ba dare ba ranan da aka sayo daga kasar Rasha

Boko Haram ta shiga uku,Najeriya ta sayi sabbin jiragen yaki daga Rasha
Boko Haram ta shiga uku,Najeriya ta sayi sabbin jiragen yaki daga Rasha

Yayinda ake cikin yaki da ta’addanci a Najeriya, rundunar sojin sama ta sayi jirage masu saukar angulu guda 2 daga hannun kasar Rasha.

A wata hira da manema labarai ranan juma’a, 6 ga watan Junairu, shugaban rundunar soji sama Iya Staff Sadique Abubakar yace : An rigaya da kai jiragen, abinda ake jira kawai rantsar da su ne domin fara artabu.

KU KARANTA: An sallami yan sanda shida akan zaben Ribas

Jaridar Premium times ta bada rahoton cewa jirage masu saukar angulun mugayen jirage ne wacce ke aiki ba dare ba rana komin rashin kyau na yanayi.

“Bugu da kari, kamfanin NNPC ta baiwa rundunar Sojin sama jirage mau sauka anguku 3x EC-135 guda uku. Da hadin kan kamfanin Aero Contractors , an gyara 2 daga cikin su kuma an fara aiki. Wannan ya kunshi NAF 547 da NAF 548.”

A shekarar 2016, an kashe sama da N25 billion akan horar da direbobin jirgin sama gida da wajen najeriya.

“Hukumar ta horar da hafsoshi 869 wanda ya kunshi direbobin jirgin sama 101 da injiyoyi 357,yayinda kuma an horar da sauran a gida.”

https://www.facebook.com/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel