Karanta adda Diezani ta saci $513miliyan

Karanta adda Diezani ta saci $513miliyan

- Tsohuwar ministar albarkatun mai ta Nigeria Diezani Alison-Madueke ta mika wa gwamnatin kasar dalar Amurka miliyan 153 da ake zargin ta sata daga asusun gwamnati.

- Hakan dai ya biyo bayan wani hukunci da wata kotu ta yanke a birnin Legas ranar Jumu'a cewa matar ta mika wadannan kudaden ga gwamnatin har a tabbatar da halaccinsu ko akasin haka.

Karanta adda Diezani ta saci $513miliyan
Karanta adda Diezani ta saci $513miliyan

A cikin bukatar neman mika kudaden wadda jami'in bincike na hukumar ta EFCC Moses Awolusi ya gabatar wa kotun, hukumar ta ce a watan Disamba na shekara ta 2014 ne tsohuwar ministar ta kira babban manajan daya daga cikin bankunan a ofishinta suka tsara yadda za a saci kudaden.

Jami'in hukumar ya yi zargin cewa Mrs Diezani Alison-Madueke ta bukaci babban manajan bankin da ya tabbatar da cewa ba a saka kudin a cikin asusun da aka san da zamansa ba kuma ba a rubuta shigar da kudin ba cikin kundin da bankin ke rubuta huldodin da ya yi ba.

Rahoton na kamfanin dillancin labaran Najeriyar dai bai fadi ko lauyoyin tsohuwar ministar suna a kotun lokacin wannan zaman ba; balle martanin da suka mayar ga wadannan zarge-zargen.

Amma dai wannan ba shi ne karon farko da ake zargin ministar da almundahana ko facaka da kudaden jama'a ba, amma kuma a kodayaushe takan musanta.

Ku biyo mu a Fezbuk: https://web.facebook.com/naijcomhausa/?_rdr

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel