Rundunar yan sanda ta sallami ma'aikata 6 kan zaben Rivers

Rundunar yan sanda ta sallami ma'aikata 6 kan zaben Rivers

- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sallami jami'anta guda shida wadanda ta ce sun aikata laifuka daban-daban a lokacin zaben 'yan majalisu da aka gudanar a jihar Rivers

- Kakin rundunar Don Awunah ya ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa jami'an wadanda suka hada da Sufeto Eyo Victor da Sajen Peter Ekpo da Sajen Ogoni Goodluck sun yi harbi cikin jama'a ba bisa ka'ida ba

Rundunar yan sanda ta sallami ma'aikata 6 kan zaben Rivers
Rundunar yan sanda ta sallami ma'aikata 6 kan zaben Rivers

Sauran sun hada da Sajen Orji Nwoke da Sajen Okpe Ezekiel da kuma Sajen Tanko Akor.

Ta kara da cewa sun aikata laifin ne ranar 10 ga watan Disambar 2016 lokacin da suka bi tawagar Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, wajen dirar mikiya a kan sakatariyar karamar hukumar Fatakwal.

Sanarwar da Mista Awunah ya fitar ta ce jami'an sun hana kai sakamako inda hukumar zabe ta tanada daga rumfar zabe ta Umouha yayin zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar.

Ta kuma ce 'yan sandan sun nuna rashin biyayya ga manyan jami'an 'yan sandan da ke wurin a lokacin.

Rundunar ta 'yan sandan Najeriya ta kara da cewa sai da aka gudanar da bincike a kan lamarin kafin a dauki matakin korar jami'an.

Bayan ta sallame su daga aiki, rundunar ta ce za ta gurfanar da su a gaban kuliya a karkashin dokar zabe domin hakan ya zama darasi ga sauran 'yan sanda.

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriyar, Idris Ibrahim, ya ce a shirye rundunarsa ta ke domin gudanar da aikinta yadda tsarin mulki ya tanada lokacin zabe da kuma bayansa.

Zaben na jihar Rivers dai ya haifar da zafafan kalamu tsakanin jami'iyyar PDP mai mulkin jihar da kuma APC wacce ke adawa.

An kuma samu hasarar rayuka da dama a rigingimun da aka yi masu alaka da zaben.

Ku biyo mu a Fezbuk: https://web.facebook.com/naijcomhausa/?_rdr

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel