Aisha Buhari ta wanke kan ta daga zargi

Aisha Buhari ta wanke kan ta daga zargi

– Matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wanke kan ta daga zargi

– An zargi Aisha Buhari da amfani da dukiyar Gwamnati wajen sha’anin ta

– Shugaban kasa ya taba cewa da kudin ta take yawo ba na al’umma ba

Aisha Buhari ta wanke kan ta daga zargi
Aisha Buhari ta wanke kan ta daga zargi

Jaridar Sahara Reporters ta fito da wasu takardu da ke nuna yadda Matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta ke facaka da dukiyar Kasa wajen tafiye-tafiyen ta zuwa Landan. Sai dai Uwargidan shugaban Najeriyar tayi wuf ta karyata wannan zargi.

Matar shugaban kasar tace karya ake yi da aka ce tayi amfani da kudin jakadancin Kasar Ingila wajen tafiye-tafiyen ta. A wata takarda da aka bayyana an nuna cewa shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Abba Kyari ya saka hannu a takardun da aka rika daukar dawainiyar matar shugaban Kasar.

KU KARANTA: Ina 'Yan Matan Chibok?

Uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari ta fito ta bakin wata mai ba ta shawara, Misis Adebisi Ajayi inda ta karyata wannan maganganu. Tayi bayani cewa Ofishin jakadancin Kasar ba su taba bata wata alfarma ba. Aisha Buhari tace ko Direbobin ta, ita ta ke kula da su, ta dai kalubancin Sahara Reporters su kawo hujja ba bata mata suna ba.

Wannan makon ne Kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya ta yabawa Hajiya Aisha Buhari inda tace tayi abin a jinjina mata da har ta bayyana ra’ayin ta game da abubuwan da ke faruwa. Shugaban Kungiyar na Kasar yarbawa ya bayyana haka Bishof M. Atilade ya bayyana haka.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel