Obama ya saki wasu fursunonin Guantanamo 4

Obama ya saki wasu fursunonin Guantanamo 4

- Ana saura kwanaki kalilan da sauka daga karagar mulki, shugaba Obama ya saki fursunoni 4 daga gidan yarin Guantanamo

- Wadanda aka sake sune Salem Ahmad Hadi Bin Kanad, Muhammed Rajab Sadiq Abu Ghanim, Abdallah Yahya Yusif Al-Shibli, da Muhammad Ali Abdallah Muhammad Bwazir

- Shugaba mai jiran gado,Donald Trump yayi Allah wadai da wannan abu

Obama ya saki wasu fursunonin Guantanamo 4
Obama ya saki wasu fursunonin Guantanamo 4

A jiya Alhamis, 5 ga watan Junairu, shugaban kasan Amurka, gwamnatin Barack Obama ta sanar da cewa zata saki ursunonin Gwantanamo 4 wanda Donald Trump yayi Allah wadai da wannan.

Fursunonin da aka saki yan kasan Yemen ne kuma yace kai su kasar Saudiyya ,akwai sauran fursunoni sama da 50 a Guantanamo.

Game da cewar ma’aikatar tsaron Amurka. Wadanda aka saki sune Salem Ahmad Hadi Bin Kanad, Muhammed Rajab Sadiq Abu Ghanim, Abdallah Yahya Yusif Al-Shibli, da Muhammad Ali Abdallah Muhammad Bwazir.

KU KARANTA: Anyima fursunoni 10,000 afuwa

Jawabin ma’aikatar tace: Kamar yadda shugaban kasa ya bada umurni a Junairun 2009, akan duba yadda za’a sake duba zancen fursunonin. Bayan an duba abubuwan an amince a saki wasu fursunonin.

Amma, shugaban kasa mai jiran gado, Donald Trump, yace kada a sake fitar da wani fursuna daga gidan yarin Guantanamo Bay dake kasar Kuba.

“Kada a sake fito da mutane daga Gitmo. Wadannan mutane ne asu hadari kuma kada a bari ku koma cikin jama’a."

A bangare guda, hukumar sojin Amurka ta amincewa soji musulmai su bar gemu ,kuma mata sun sanya hijabinsu.

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel