2016: Ko kasan wanda yafi kowa iya kwallo a Afrika?

2016: Ko kasan wanda yafi kowa iya kwallo a Afrika?

- Dan wasan gaba na Algeria Riyad Mahrez shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na CAF na 2016

- Mahrez wanda ya ke yi wa Leicester City wasa a gasar Premier ya taka muhimmiyar rawa a kofin gasar Premier da kungiyar ta dauka a kakar da ta wuce, inda ya ci musu kwallo 17

2016: Ko kasan wanda yafi kowa iya kwallo a Afrika?
2016: Ko kasan wanda yafi kowa iya kwallo a Afrika?

A watan Disambar da ya gabata, Mahrez ya samu kyautar gwarzon dan wasan Afirka na BBC na 2016.

A bangaren mata kuwa, Asisat Oshoala 'yar Najeriya ita ce ta zama gwarzuwar 'yar wasan kwallon kafa ta Afirka ta 2016 ta CAF.

An gudanar da bikin raba kyautukan ne a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

A shekarar 2015 dai Pierre-Emerick Aubameyang ne ya lashe kyautar ta CAF.

Kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta 2016

1. Riyad Mahrez (Algeria da Leicester City) - Kuria 361

2. Pierre-Emerick Aubameyang (Gabon da Borussia Dortmund) - Kuria 313

3. Sadio Mane (Senegal da Liverpool) - Kuria 186

Ku biyo mu a Fezbuk: https://web.facebook.com/naijcomhausa/?_rdr

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel