Wata Kungiyar Kabilar Igbo ta ce mulkin Buhari ya fi kowanne ga mutanen Kudu Maso Gabas

Wata Kungiyar Kabilar Igbo ta ce mulkin Buhari ya fi kowanne ga mutanen Kudu Maso Gabas

Wata kungiyar ‘yan kabilar Igbo ta duniya mai suna Igbo World Union (IWU), ta ce mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana yin abin da ya dace ga yankin kudu maso gabas.

Wata Kungiyar Kabilar Igbo ta ce Mulkin Buhari ya fi Kowanne Ga Mutanen Kudu Maso Gabas
Wata Kungiyar Kabilar Igbo ta ce Mulkin Buhari ya fi Kowanne Ga Mutanen Kudu Maso Gabas

Kungiyar kuma tace mulkin Buhari shine wanda yafi kowanne mulki ga "yan kabilar ta Igbo, kamar yanda jaridar Nigerian Tribune ta rawaito.

Da yake magana Gburugburu Ndi Igbo na uku a farfajiyar Dum a garin Umuajata-Olokoro cikin Umuahia da ke kudancin jihar Abia, a yayin bikin shekara na Ofala, wanda ya kirkiro kungiyar ta IWU, Mishak Nnanta, yayi kira ga "yan kabilar ta Igbo da su farka daga baccin da suke tare cike gurbin da yace a Najeriya.

A cewar jaridar Nigerian Tribune, Nnanta, ya yi kira ga gwamnonin kudu maso gabas da su daina sa siyasa cikin abinda ya shafi cigaban yankin.

Ya kuma yi kira ga ‘yan kabilar ta Igbo da su hada hannu da gwamnati wajen ayyukan cigaban kasa.

Ya ce: "Har yanzu Igbo sun gaza cimma burinsu, duk da cewa mune "ya "yan farko a Najeriya. Matsalolin mu suna tafukan hannayen mu. Mu kaucewa yunkurin raba kai. Mu rungumi hadin kai. Idan muka dage cewa sai mun balle daga Najeriya, saboda me muke san barin ta?"

Duba da cibaya da al'ada da harshen Igbo suke, ya nuni da cewa: "Kyawawan dabi'u da shiga ta mutunci an watsar da su zuwa kwandon shara, an rungumi al'adun mutanen waje na shiga ta nuna tsaraici.

Kungiyar IWU a matsayin ta na kungiyar al'ada tanayin duk mai yiwuwa wajen ganin an tattala tare da bunkasa kyawawan dabi'un Igbo tare da kawar da hankalin jama'a daga barin bakin al'adu ta hanyar farfado da dabi'u na gari, harshe da kuma kimar yaren ta yanda "yan baya zasu tarar dasu an killace musu," inji shi.

Har yau dai ya ci gaba da cewa: "IWU na kuma nufin nunawa Ndigbo, al'adun su, tsarin rayuwar su da kuma abinda suka gada na mutunci ga duniya da nufin sauya kallon da akewa kabilar Igbo dama Najeriya tare da jawo hankalin duniya zuwa kyawawan al'adun wanda zai sa masu yawan bude idanu su dinga kawo ziyara zuwa yankin wanda kuma zai kawo fa'ida ga kabilar Igbo dama Najeriya baki daya."

A lokaci guda kuma, wani gangamin rajin dimukradiyya wanda ba na gwamnati ba, yayi ikrarin cewa, a kalla matasa dubu-biyu ne "yan kabilar ta Igbo sojojin Najeriya suka kashe da sunan aikin kwantar da tarzoma.

Ku biyo mu a shafimu na Facebook a https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da kuma Tuwita a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel