Mayakan Boko Haram 20 sun mika wuya ga sojoji a Nijar

Mayakan Boko Haram 20 sun mika wuya ga sojoji a Nijar

- Gwamnatin Nijar tace kimanin yan ta’addan kungiyar Boko Haram 20 ne suka mika wuya bayan yan ta’adda 50 da suka mika wuya a baya

- Rikicin ya mayar da kimanin mutane miliyan 2.6 marasa galihu

- Diffa ya kasance daya daga cikin yankuna mafi muni, tare da kimanin mutane 300,000

Gwamnatin Najeriya ya bayyana cewa kimanin mutane 20 na yan ta’addan kungiyar Boko Haram ne suka mika wuya bayan yan ta’adda 50 da suka mika kansu ga hukumar tsaro a baya.

“Kimanin mayakan Boko Haram 50 ne suka mika kansu” tun ranar 27 ga watan Disamba, ministan harkokin cikin gidan Nijar, Bazoum Mohamed, ya bayyana hakan a wani hira a daren ranar Laraba, 4 ga watan Disamba, a gidan talbijin din Channel Tele Sahel.

Mayakan Boko Haram 20 sun mika wuya ga sojoji a Nijar

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali a jihar Niger: Makiyaya sun kashe mutane 400, sun kuma sace mata da dama

Mohamed ya alakanta nasaran da wani hari da yan bindigan suka kai a kan kungiyar a watan Yuli da kuma kulawan jami’an tsaro a Najeriya da Chadi.

An kashe sojojin Nijar uku da kuma raunata mutun bakwai a daren sabuwar shekara lokacin da yan Boko Haram suka kai harinsu a Baroua, a yankin Diffa, cewar sojin. An kashe yan bindiga goma sha biyar an kuma kama wani guda daya, cewar sa.

Kungiyar Boko Haram na neman shekaru na bakwai a kan Najeriya wanda ya ci sama da rayuka 20,000, tare da yan ta’addan da suka rarrabu a fadin iyakokin kasashen Afrika maso yamma zuwa jihohin makwabta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel