‘Yan kabilar Igbo suna da duk abin da bukata don zama masu fada aji a Siyasar Najeriya – Shugaban Ndigbo

‘Yan kabilar Igbo suna da duk abin da bukata don zama masu fada aji a Siyasar Najeriya – Shugaban Ndigbo

- Kabilar Igbo na da duk abinda ake nema don zama masu fada aji a siyasar Najeriya, a cewar wani shugaban Ndigbo

- Shugaban na kabilar Igbo mai suna, Peter Chibueze Chukwu, daga jihar Delta, ya yi kira ga’yan kabilar Igbo da su daina korafin nuna musu wariya, ya kara da cewa, ya kamata su ga yawan da suke da shi a matsayin karfin da zai ba su dama ayi duk wata yarjejeniyar siyasa da su

‘Yan kabilar Igbo suna da duk abin da bukata don zama masu fada aji a Siyasar Najeriya –Shugaban Ndigbo
‘Yan kabilar Igbo suna da duk abin da bukata don zama masu fada aji a Siyasar Najeriya –Shugaban Ndigbo

Eze Chukwu, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a garin Warri na jihar Delta a ranar Litinin 3 ga watan Janairu, ya yi nuni da cewar, kabilar Igbo su ne ke mai da kansu baya a siyasar Najeriya.

Ya kara da cewa, yankin na da duk abin da ake bukata dan samun bakin fada aji a siyasar Najeriya.

a ce: " Mutanen mu har yanzu ba su rabu da tasirin yakin basasa ba, sanda sojoji suka wawantar da hankulan mu ta hanyar mai da "yan uwan mu Igbo na yakar juna sannan su ka zabi goyon bayan wasu shugabannin bogi a tsakanin Igbo."

"Kabilar Igbo, ba'a danne su ba, sannan wadanda suke ji an danne su yakamata su sauya tunani," in ji shi.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tattaunawa a kan batun Shugaban "yan taware na kabilar Igbo, wato Nnamdi Kanu, wanda yanzu haka ya ke fuskantar tuhumar cin amanar kasa.

Yayi nuni da yadda a shekarar 1964, aka tuhumin Isaac Adaka Baro, da kuma Chief Obafemi Awolowo da laifin cin amanar kasa daga baya a shekarar 1966 aka yafe musu.

Ya kara da cewa: "Wadannan mutane daga baya sun bada gudunmawa wajen gina kasa ta fannoni daban-daban. Isaac Adaka Baro daga baya ya zama jaruman soja, shi kuma Awolowo daga baya ya zama Ministan kudi, kuma ya bada gagarumar gudunmawa," ya kara da cewa ya kamata ita ma gwamnantin Buhari ta baiwa Nnamdi Kanu irin wannan dama."

A lokaci guda kuma kungiyar "yan asalin Biafra wato IPOB, ta yi zargin cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana da wani boyayyen gurin tsare mutane wanda hukumar "yan sandan farin kaya ke kula da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel