Kasar Somalia ta karrama yansandan Najeriya 136 da lambar yabo

Kasar Somalia ta karrama yansandan Najeriya 136 da lambar yabo

Jami’an hukumar yansandan Najeriya su 136 suka samu lambar yabo daga gwamnatin kasar Somalia bayan sun kammala wa’adinsu na gudanar da aikin kwantar da tarzoma.

Kasar Somalia ta karrama yansandan Najeriya 136 da lambar yabo
Kasar Somalia ta karrama yansandan Najeriya 136 da lambar yabo

Yansandan sune rukuni na 5 da aka aika zuwa kasar Somalia don gudanar da aikin kwantar da tarzoma a karkashin tsarin kwamitin tsaro na tarayyar kungiyar kasashen Afirka.

Wata sanarwa daga kamfanin dillancin labarai tace yansandan Najeriya su 136 ne suka fafata a faretin bada lambar yabo daya gudana a ranar Talata 3 ga watan Disamba.

“mataimaki na musamman ga kwamishinan yansandan hadakar kasashen Afirka dake aiki a Somalia ne ya jagoranci taron karrama yansadan. Shima shugaban yansandan kasar Somalia Janar Mohamed Sheikh Hassan Hamud ya samu halartan taron tare da tawagarsa.”

KU KARANTA:Gwamnatin tarayya ta mayar da martani ga gwamna Ayo Fayose

Shugaban ayyukan tsaro na musamman na majalisar kasashen Afirka a Somalia, Lydia Wanyoto tagode ma gwamnatin Najeriya dangane da irin goyon bayan data basu tare da kokarin samar da zaman lafiya a Somalia. Sa’annan ta bayyana godiyarta ga jami’an tsaron kasar Somalia da suka halarci taron.

Tace: “Mun zo taron nan ne saboda kasar Somalia, kuma a madadin kasar Somalia. Ina mika godiyata gareku saboda aikin da kuka yi, mun gode muku da kuka sadaukar da rayukanku don kare mutanen kasar Somalia.”

Shima shugaban hukumar yansandan kasar Somalia Janar Hamud ya yaba ma yansandan Najeriya musamman wajen tabbatar da doka da oda a kasar. Hamud yace, “kun kasance jakadu na gari ga kasarku. Somalia ba zata taba mantawa da Najeriya ba”

A wani labarin kuma Babban hafsan mayakan sojojin kasa laftanar janar Tukur Buratai ya bayyana cewar zasu aika da dakarun sojojin kasa har su 800 zuwa yankin Darfur a karkashin shirin majalisar dinkin duniya na kwantar da tarzoma (UNAMID).

zaku iya samun labaran mu a www.twitter.com/naijcomhausa www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel