Gadoji 6 da gwamnatin tarayya za ta gyara a shekarar 2017.

Gadoji 6 da gwamnatin tarayya za ta gyara a shekarar 2017.

- Gine-gine kamar su gadoji da su ke takaita wahalhalu ba tare da rufe hanya ba na da matukar muhimmanci

- Daya daga cikin matsalolin da gine-gine da kayayyakin da gwamnati ke samarwa shi ne kula da su. Ba a tabuka abin a zo a gani wajen ganin gine-ginen ba su lalace ba

Gadoji 6 da gwamnatin tarayya za ta gyara a shekarar 2017.
Gadoji 6 da gwamnatin tarayya za ta gyara a shekarar 2017.

Tsarin da a ke amfani da shi ya fi mayar da hankali wajen samarwa ba kula da su ba. Amma lokaci ya zo da za a gyara wasu gadoji a kasar nan. Yayin da kila gwamnati ke farkawa daga bacci da wannan shawara ta gyara wadannan gadoji, ya na da muhimmanci a wayar wa da jama'a kai. Ya kamata 'yan Najeriya su san rawar da ya kamata su taka wajen kare kadarorin kasa.

Gwamnati ta shirya kashe makudan kudade wajen riritawa da dawowa da kuma gyara sama da gadoji 50 a kasar nan farawa daga wannan shekara.

Dubi 6 daga cikin gadojin da za gyara a 2017:

1. Titin ring round da ta zagaye jihar Lagos.

Gadar ta hada Mainland zuwa Victoria Island da Ikoyi.

Gwamnati ta shirya ta fara aiki a kan manyan gadoji zuwa kanana. Wannan zai kare su daga rugujewa kuma zai rage kashe kudi sosai.

2. Gadar tsibirin Mainland ta uku a Lagos ita ce mafi tsahon gada da ta hada Lagos Island zuwa Mainland. Gadar ta taba zama mafi tsaho a Afirka har lokacin da a ka gina gadar 6th October a Cairo. Tsahon gadar ya kai kimanin kilomita 11.8, ta fara daga Oworonshoki ta tsaya a Adeniji Adele Interchange a Lagos Island.

Mutane da yawa su na amfani da gadar kullum kuma ya na da muhimmanci a dinga kula da ita a kai a kai.

3. Gadar Jaji a Kaduna

Wannan gada ta na kan hanyar Kaduna zuwa Zaria. Kamfanin Borini Prono a ka bawa aikinta.

4. Gadar Tamburawa a Kano.

Wannan gada ta na tsakanin Kaduna da Kano amma mafi yawanta ta na Kano ne. Gadar ta dade ta na fama da fashewa da rauzayewa. Harkokin hakar ma'adanai a wajen ne ke kara fito da sassanta. Ya na da kyau a gyara wannan gada a mayar da ita kusa da yadda ta ke a da.

5. Gadar Apapa a Lagos

Ya na daga cikin Kudurorin gwamnati gyaran gadar Apapa tun da dadewa. Gadar ta kai shekara 40 amma ba a taba yi mata gyaran da ya kamata a yi mata ba.

6. Gadar kogin Niger ta biyu

Wannan gada ta na taimakawa gadar kogin Niger wajen hada sashin yamma zuwa Gabas.

Idan a ka gyara wadannan gadoji, a na sa ran sufuri zai bunkasa kuma rasa rayuka a sanadiyyar hadura zai ragu.

Ku biyomu a dandalin Facebook a www. facebook.com/naijcomhausa da kuma Tuwita a www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel