An damke Sojan bogi mai satan babura a Legas

An damke Sojan bogi mai satan babura a Legas

Hafsan hulda da mutane na hukumar yan sanda jihar Legas, Dolapo Badmus ta tabbatar da wannan

An damke Sojan bogi da satan babura a Legas
An damke Sojan bogi da satan babura a Legas

Jami’an yan sandan Special Anti-Robbery Squad (SARS) damke wani Wani Sojan bogi wanda ya kasance yana satan baburan mutane a jihar Legas.

Sojan bogin mai suna Benjamin Okon,ya kasance yana kiran kansa Soja. Yan sanda sun bisa sun kama shi bayan sun samu rahoto daga wurin mutane a ranan Lahadi,1 ga atan Junairu 2017 ,karfe 5 na yamma.

KU KARANTA: Dalibin jamía ya hallaka kansa

Wata majiya tace: “Mutumin ya kasance yanayima mutane unguwa barazana akan cewa shi Soja ne. wannan hali nasa ne ya sanya mutane basu hulda da shi. Amma lokacin da muka gano take-takensa,sai muka kai kara wajen yan sanda.”

Benjamin Okon,wanda ya tona asirin kansa lokacin wani bincike cewa: “Ni kwararren mai kwace baburan mutane ne. na sace Babura da dama, wanda akwai wanda mukeyi tare shine mai sayar da su. Ina tafiya ko ina a fadin kasan nan domin yin wannan abu. Idan na kawo masa babur, sai ya biya ni,sai in je in sato wani.”

Hafsan hulda da mutane na hukumar yan sanda jihar Legas, Dolapo Badmus,wacce ta tabbatar da abun tace za’a kaishi kotu idan an karasa bincike.

Hakazalika irin wannan abu ya faru a jihar Ondo inda wani sojan bogi mai suna Mike Ajulo yake fakewa da soja a karamar hukumar Ose.

https://www.facebook.com/naijcomhausa

https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel