Rundunar sojin Gambia ta bayyana goyon bayantar ga Jammeh

Rundunar sojin Gambia ta bayyana goyon bayantar ga Jammeh

- Dangane da barazanar da aikawa dakarun sojai da ECOWAS ta yi wa shugaba Jammeh, shugaban rundunar sojin Gambia, Ousman Badjie ya nuna goyon baya ga shugaban

- Badjie ya jaddada biyayya da goyon bayan rundunar soja ga Jammeh a wata wasika da ya aikewa jarida mai goyon bayan gwamnati, Daily Observer.

Rundunar sojin Gambia ta bayyana goyon bayantar ga Jammeh
Rundunar sojin Gambia ta bayyana goyon bayantar ga Jammeh

Akwai kwararan alamu cewa Gambia ka iya fadawa cikin yaki biyo bayan rikici kan sakamakon zabe.

Rundunar sojin Gambia ta kalubalanci ECOWAS, inda ta jaddada goyon baya ga shugaba Yahaya Jammeh. Biyo bayan barazanar daukan matakin soja da shugaba Muhammadu Buhari da wasu shugabannin ECOWAS su ka yi, shugaban rundunar sojin Gambia Ousman Badjie ya jaddada biyayyarsa ga shugaba Yahya Jammeh.

BBC ta rawaito cewa, a wata wasika da ya aika wata jaridar kasar mai goyon bayan gwamnati, Daily Observer, Badjie ya jaddada biyayya da goyon bayan daukacin sojojin Gambia ga Jammeh. Jammeh ya dage cewa, ba zai sauka ba in wa'adinsa ya kare ranar a 19 ga watan Janairu.

Ya kuma rubuta:

"Zan yi amfani da wannan dama na sabunta tabbacin biyayya da goyon bayan rundunar sojin Gambia ga mai girma shugaban kasa."

Idan mista Jammeh ya ki mika mulki ga shugaba mai jiran gado, Adama Barrow a ranar 19 ga watan Janairu, ECOWAS ta ce, sojojinta a makwabciyar kasar Sanegal a shirye su ke su kawo dauki a yanayin siyasar Gambia.

Idan za a tuna tun farko sai da shugaban Gambia ya amince ya sha kaye a zaben da a ka gudanar ranar 1 ga watan Disamba shekarar 2016, amma ya canja shawara daga baya.

Shugaban ya yi gargadi da cewa, duk wani yunkuri na yin katsalandan a siyasar kasar zai zama 'takalar yaki ne.'

BBC ta kuma rawaito cewa kasar ba ta samu canjin gwamnati ba tun samun 'yancin kai daga Burtaniya a 1965.

Shugaban hukumar zaben Gambia ya tsere zuwa Senegal ya na zargin barazana ga rayuwarsa.

Ku biyomu a dandalin Facebook a www.facebook.com/naijcomhausa da kuma Tuwita a www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel