Makiyaya sun yi barna a jihar Neja

Makiyaya sun yi barna a jihar Neja

– Fulani Makiyaya sun yi uban ta’asa a jihar Neja

– An kashe Mutane da dama an kuma sace ‘yan mata a yankin a shekarar bara

– Sanata David Ummaru na yankin ya bayyana haka

Makiyaya sun yi barna a Jihar Neja
Makiyaya sun yi barna a Jihar Neja

Fulani Makiyaya ba karamar ta’asa suka yi ba a Jihar Neja inji wani Sanata mai wakiltar Bangaren Gabashin Jihar. Sanata David Ummaru yace Fulani Makiyaya da ‘Yan Iskan Garin sun kashe mutane har 400 a shekarar da ta gabata watau 2016.

Sanatan yayi magana ne da ‘yan jarida inda yake bayanin yadda lamarin tsaro ya tabarbare a Yankin. Sanata Ummaru shine Shugaban Kwamitin shari’a da kare hakkin bil’adama a Majalisar Dattawar Kasar. Yace wadannan mutane ka zo da manyan Bindigogi, suna nan a Dajin da ya rabi Kaduna da Neja.

KU KARANTA: Sanata ya caccaki dan uwan sa

Ko a kwana-kwanan nan, Jiya Laraba dai wasu ‘Yan Iskan Garin sun kara sace wasu ‘Yan matan tare da yin lalata da wasu. Har wa yau kuma an yi gaba da shanu da dama. An dai yi asara ta makudan miliyoyi. An dai nemi Gwamnati ta dauki mataki kan lamarin.

A shekaran jiya ne Shugaban Kasa yayi gargadin cewa har yanzu fa da sauran rina a kaba wajen Yaki da ta’addanci. Shugaba Buhari yake cewa ‘Yan Kasa su bi a hankali don a ko yaushe ana ‘yan ta’addan na iya kawo hari duk da an ci karfin ‘Yan Boko Haram har a Gidan su.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel