Wani Saurayi ya caka ma wata mata wuka saboda ta karanta ‘Bible’

Wani Saurayi ya caka ma wata mata wuka saboda ta karanta ‘Bible’

Wani matashin mai shekaru 22 ya caka ma wata mata yar addinin kirista mai shekaru 50 wuka saboda ya jiyo ta tana karanta littafin ‘Bible’.

Wani Saurayi ya caka ma wata mata wuka saboda ta karanta ‘Bible’
‘Bible’

Wannan lamari ya faru ne a garin Timelkam, Voecklamarkt dake arewa maso kudancin kasar Austria. Rahotanni sun bayyana cewar matashin ya harzuka ne saboda matar ta shigo dakinsu tana karanta Bible a bisa gayyatar da aka yi mata don tattauna littafin.

KU KARANTA:Yadda aka yi bikin shiga sabuwar shekara a Legas

Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewar yayin da saurayin ya saurari abinda matar ke karantawa, sai ya bita cikin dakin girki wato kitchen, inda yayi kokarin caka maka wuka a kirjinta, sai dai bai samu nasara ba, amma fa matar ta samu rauni a kunnenta sakamakon faduwa da tayi ta baya.

Yayin da yansanda suka tambaye shi kan dalilinsa na aikata haka, sai Saurayi ya amsa laifinsa, inda yace ya san ya wuce gona da iri, amma ayi mai afuwa, saboda yana fama da matsalar da shi kadai ya san abinda ke damunsa.

A yanzu dai an garzaya da shi gidan yarin garin Wels, sai dai ba tabbatar da ko an gurfanar da shi gaban kotu ba.

Ku cigaba da bibiyan mu a nan ko a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel