Leicester City ta sake siyan dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi

Leicester City ta sake siyan dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi

Zakarun gasar cin kofin firimiya ta kasar Ingila wato Leicester City ta sanar da kammala siyan dan wasan Najeriya mai shekaru 20 akan kwantaragi na tsawon shekaru biyar.

Leicester City ta sake siya dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi
Wilfred Ndidi

Leicester ta sayi Ndidi ne daga kungiyar Genk dake kasar beljam, tuni aka gwada lafiyar Ndidi a kungiyar Leicester, abin da yake jira yanzu kawai shine samun izinin buga wasa kasar Ingila.

KU KARANTA:Olivier Giroud ya ci ma Arsenal wata mahaukaciyar kwallo da bayan kafa (bidiyo)

Ndidi ya wakilci Najeriya a gasar cin kofin yan kasa da shekaru 17 da 20, sa’annan ya samu gayyata don buga ma Super Eagles a watan Oktobar 2015, inda yayi wasa tare da shahararren dan wasan Leicester kuma dan Najeriya Ahmed Musa.

Komai lafiya lafiya Ndidi zai cigaba da buga wasa a Leicester har zuwa shekarar 2022.

Ku cigaba da bibiyan labaran mu a nan ko a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel