Gwamnatin jihar Sakkwato zata gudanar a jarabawa ga malaman makaranta

Gwamnatin jihar Sakkwato zata gudanar a jarabawa ga malaman makaranta

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yace gwamnatin jihar sa zata gudanar da jarabawa ga dukkan malaman da ke koyarwa a makarantun jihar Sakkwato.

Gwamnatin jihar Sakkwato zata gudanar a jarabawa ga malaman makaranta
Gwamnatin jihar Sakkwato zata gudanar a jarabawa ga malaman makaranta

Gwamnan ya bayyana hakan lokacin da ya gana da shugaban kwamitin akan ilimi ,Farfesa Risqua Arabu Shehu.

Kwamitin zata gabatar da rahoto ga gwamnatin jihar akan abubuwan da ake buka na kuntata makarantu da akayi a watan Nuwamban da ya gabata.

Jawabin ta fito ne daga hannun mai Magana da yawun Tambuwal,Malam Imam Imam, inda yace za’a gudanar da jarabawan ne saboda tabbatar ilimin malamai bisa ga bukatun ilimin ,da kuma sanin inda za’a turasu.

"Jarabawan zai taimaka wajen sanin yawan malaman da ke koyarwa a makarantan gwamnati wanda zai bada ikon ajiye takardun su a hukumomin gwamnati."

Amma wannan ba wai yana nufin cewa wadanda suka fadi jarabawan za’a koresu ba. A’a kawai za’a canza musu wajen aiki da yayi daidai da su. Gwamnati zasu cigaba da amfana da su.

Tambuwal ya sha alwashin cewa, gwamnatinsa bazata gushe tana kokarin bunkasa ilimi a jihar sakkwato ba.

" Wannan shi yasa a kasafin kudin 2017, ilimi yafi samun kudi cikin kasafin. Tunaninmu shine komin yawan kudin da aka tura bangaren ilimi bai yi yawa ba.”

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel