Hankalin gwamnatin tarayya ya tashi akan rikicin Musulmai da Kirista

Hankalin gwamnatin tarayya ya tashi akan rikicin Musulmai da Kirista

- Akwai tashin hankali game da yaki tsakanin Musulmai da Kirista a Najeriya

- Archbishop Benjamin Kwashi yace Boko Haram da makiyaya zasu sabbaba yaki tsakanin musulmai da kirista

- Gwamnatin tarayya tayi gargadi ga malamai akan tayar da hankalin jama’a

Hankalin gwamnatin tarayya ya tashi akan rikicin Musulmai da Kirista
Hankalin gwamnatin tarayya ya tashi akan rikicin Musulmai da Kirista

Most Rev Benjamin Kwashi yayi gargadi kan cewa da yiwuwan a samu yaki tsakanin mabiya addinin Islama da Kirista a kasan nan. Yace dalilin haka shine hare-haren da ake kaiwa kiristoci a wannan kasa kwanakin nan.

Shugaban fastocin Jos din yace wasu yan tsattsauran addini irin Boko Haram da Makiyaya sun acigaba da cin mutuncin mabiya addinin kirista a arewacin Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar sakkwato zata gina makarantun Boko hade da Islamiya

Ya bayyana hakan ne yayinda yake Magana fa kungiyar Christian anti-persecution charity Release International, yace ya kasa fadawa mabiya addinin kirista su zauna a arewa saboda rayuwansu na cikin hadari,amma idan suka zabi zama a wurin, su dogara da Allah.

Malamin addinin kiristan ya tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya tayi kokari waje fitittikan yan Boko Haram, amma har yanzu bata kare rayuwan kiristoci da Fulani makiyaya ba.

Yace babu gwamnan arewan da ya damu da kiristoci, da akwai,da ba za’a dinga cin mutuncinsu ba,,da a kare su.

Yace: “Kiristoci sun fidda tsammani kuma sunyi fushi. Allah kadai ya san abinda yasa basu rama ba. Amma idan suka fusata,akwai matsala.

"Idan gwamnatin tarayya ta bari mutane suka fara daukan hukunci a hannunsu,zasu kairamuyar gayya wata rana.”

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel