Wani mutumi ya kashe kansa bayan ya kama matarsa da wani a kan gado

Wani mutumi ya kashe kansa bayan ya kama matarsa da wani a kan gado

Wani mutumi ya yanke shawaran kawo karshen rayuwarsa bayan ya kama matarsa abin kaunarsa rungume da wani mutumi, a gadon aurensu.

Wani mutumi ya kashe kansa bayan ya kama matarsa da wani a kan gado
Wani mutumi ya kashe kansa bayan ya kama matarsa da wani a kan gado

Bisa ga rahotanni, mutumin da aka kira da Tapiwa Shumba, ya shigo gidansu a Mwenezi, kasar Zimbabwe, zuwan bazata (yayi tafiya kuma ana sa ran zai dawo washegarin ranar), kawai sai ya tsinci matarsa a kan gado tare da wani mutumi mai suna Zelas.

Marigayi Shumba ya fita a take, ya nemi igiya ya kuma raaye kansa har lahira. Matar sa Precious Shumba, wacce danama ya isheta sakamakon mutuwar mijina ma ta rataye kanta cikin kunya.

KU KARANTA KUMA: Dole Najeriya ta rage yawan sanatoci, wakilai – Janar Momah

Ga abunda ya faru bisa ga wani makwabcinsu:

“Da ya dawo ya kwankwasa kofar uwar dakinsu amma Precious ta dade bata bude kofa ba. Sai yayi zargin wani abu don haka ya karya kofar. Lokacin da ya shiga ciki, ya samu matarsa da Zelas wanda cikin rudani ya kusa rataye kansa.”

An rahoto cewa Shumba ya dakatar da Zelas daga kashe kansa, kafin shi ya je ya kashe kansa.

“Lokacin da ta kasa bashi bayanin abunda ke faruwa, ya fita daga gidan ya barta ita kadai tunda Zelas ya gudu. Anga Shumba ya rataye kansa washegarin ranar ga mamakin kowa, wasu yan kauye suka kuma kama Precious ta rataye kanta a wannan ranan.”

Mahaifin marigayi Shumba Fanny Matambe yace:

“Har yanzu ahlin gidan na cikin jimamin dalilin da yasa apiwa da matarsa suka yanke shawarar kashe kansu. A maimakon haka dama sun sasanta kansu gashi yanzu sun mayar da yayansu marayu.”

Zelas ya gudu ya bar kauyen tun bayan afkuwar al’amarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel