Mijina ya fi karfin ku, Makiya-Inji Uwargidan Fayose

Mijina ya fi karfin ku, Makiya-Inji Uwargidan Fayose

– Matar Gwamnan Jihar Ekiti ta roki Ubangiji yak are Mai Gidan ta

– Uwargidan tayi kakkausan addu’a ga masu neman kawo tangarda

– Misis Fayose tace akwai masu jirwaye-mai-kamar wanka

Mijina ya fi karfin ku, Makiya-Inji Uwargidan Fayose
Mijina ya fi karfin ku, Makiya-Inji Uwargidan Fayose

Uwargidan Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose ta nemi Ubangiji ya kare Mijin ta ya kuma tona asirin makiyan sa. Matar Gwamnan tace akwai masu rabar Mijin ta alhali kuma ba masoyan sa bane na hakika.

Matar Gwamnan tayi addu’a dai Ubangiji ya tona asirin Makiya Mijinta masu rabar sa kamar suna goyon bayan sa alhali nema suke su soke sa ta baya. Matar Gwamnan tayi wannan addu’a ne a wani zaman coci da aka yin a karhsne shekarar nan domin nuna godiya ga Ubangiji.

KU KARANTA: Kwanakin Shugaban UN sun kare

Uwargida Feyisetan Fayose tace abin fa ya isa haka nan yanzu, asirin makiya zai tonu bana. Matar Gwamnan ta kuma yi kira da ‘Yan Jihar suyi watsi da duk wasu masu neman ganin bayan Gwamnan. Matar Gwamnan dai tace ta Allah ba ta mutum ba.

A jiya ne kuma muka samu labarin cewa Gwamnatin Jihar Ekiti ta rabawa matasa filayen noma domin rage matsalar rashin aikin yi a Jihar. Gwamnatin Jihar ta hada kai ne da wata Kungiyar noma mai suna Agro-Nigerian LTD a wani shiri mai suna ASPP na manoma.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel