Dalilin da yasa na soki abokina har lahira kan N200

Dalilin da yasa na soki abokina har lahira kan N200

- Wani mutumi mai shekaru 30 ya bayyana yadda ya soki shakikin abokinsa har lahira kan marigayin yaki biyan kudin gyaran abun wuta da ya samu matsala

- Mai laifin ya daura laifin mugun aikinsa a kan shaidan

Dalilin da yasa na soki abokina har lahira kan N200
Dalilin da yasa na soki abokina har lahira kan N200

Ndubusi Kalu, wani maigadi mai shekaru 30, ya tona asirin sukar abokinsa har lahira kan naira dari biyu (N200) a jihar Ogun.

Al’amarin ya faru ne a unguwarsu dake Saula Sanni a yankin Agbado na jihar.

Kalu, wanda aka tisa keyarsa a gaban manema labarai a ranar Litinin, 2 ga watan Janairu, ya daura laifin aikinsa a kan shaidan.

Bisa ga jaridar Daily Post, Kalu ya soki shakikin abokin nasa kuma abokin zaman sa a daki Simeon Chidi bayan yaki biyan kudin gyaran abun wuta da ya samu matsala.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali a Ilorin kan rikicin addini

Da yake bayanin yadda al’amarin ya faru, Kalu yace: “Na fada mashi akwai bukatar mu gyara wutan da ya baci a kan lokaci saboda ina son na kalli talbijin sannan na huta a gida.da muka kasa hada naira 1,000, mai gyaran wutan ya bukaci mu biya naira 500.

"Da Chidi ya kasa biyan kudin, cewa kudin na tare da wani kuma mai shi ya fita, yayi barazanan duka na da asiri idan na kuma damun sa.

“A lokacin ne muka soma musayar yawu. Ya dauki wuka ya kuma bukaci na fito waje.

“A yayinda nake cikiniyar kwace wukar daga hannun sa, ya ji mun ciwo a hannu da kafa, nima na fasa kwalba sai muka fara fada kuma.

“Mutane sun taru da yawa suna kallonmu amma babu wanda yazo raba mu.

“Sai bayan da na soke shi a baya sannan wani mutumi da ake kira Baba Sheri yazo ya raba mu. Bawai nayi niyan kashe shi bane. Sharrin shaidan ne,” Kalu ya bukaci ayi mai afuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel