Makiyaya na barazanar kwace mana fili – Shugabannin jihar Delta

Makiyaya na barazanar kwace mana fili – Shugabannin jihar Delta

- Shugabannin wani yanki a jihar Delta sun kawo kuka akan yunkurin kwace musu fili da Makiyaya ke son yi

- Sun ce ba zasu bar unguwar ba har sai idan shugaban sun a Asaba ya umurcesu su bari

Makiyaya na barazanar kwace mana fili – Shugabannin jihar Delta
Makiyaya na barazanar kwace mana fili – Shugabannin jihar Delta

Fulani makiyaya sunyi barazanar kwace filayen mazauna karamar Burutu na jihar delta, DailyPost ta bada rahoto.

Majiyoyi sun bayyana cewa wasu Fulani makiyaya wadanda sukayi ikirarin cewa shugabansu na Asaba ne ya turo su a ranan juma’a,30 ga watan Disamba,su kwace unguwan Ayakoromo.

Amma, shugabanni da dattawa unguwan sune ba zasu yarda irin wannan abu ya faru ba a garinsu.

KU KARANTA: Illar dokar shigowa da motoci ta iyakokin kasa ta fara bayyana

Dattawan sun fada wa makiyayan cewa doka bata amince da su kwace filayen mutanen ba don suna wani taro.

Amma makiyayan suka fusata, sukace sunada yancin zuwan duk inda suka ka dama da kayan kiwonsu a fadin Najeriya.

Kana sun kara da cewa zau shigo da kauyen Ayakoromo da awakansu ko da me ko dan me.

Makiyayan sun bar garin ne kawai suna sauraran umurnin shugabansu da ke Asaba. Amma wata jawabin mukaddashin shugaban kungiyar masu fafutukan Ayakoromo, Austin Ozobo da Alaowei Cleric yace wannan barazana da makiyayan sukayi ya tayar da hankalin mazauna garin.

Sunce mata na far gaban zuwa gonakinsu domin kada makiyayan suyi garkuwa da su

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel