Kwanakin Shugaban Majalisar Dinkin Duniya sun cika

Kwanakin Shugaban Majalisar Dinkin Duniya sun cika

– Ban-Ki Mon ya gama wa’adin sa a matsayin Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

– UN ta nada sabon Shugaba

– Amina J Mohammed ta Najeriya za tayi aiki a matsayin Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar

Kwanakin Shugaban Majalisar Dinkin Duniya sun cika
Kwanakin Shugaban Majalisar Dinkin Duniya sun cika

Wa’adin Tsohon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya watau UN ya kare bayan da ya shafe shekaru 10 yana kan kujera. Ban Ki Mon din ya gama aikin na sa a karshen watan Disamban bara.

Shugaban Majalisar Dinkin Duniyan, Ban Ki Mon ya gode da damar da aka basa. Ban din ya yaba da kokarin Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniyan. A lokacin Shugaban dan Kasar Korea, ya mayar da hankali kan harkar gyara yanayin Kasa da matasa da kuma daidata jinsi da dai sauran su.

KU KARANTA: Gobara ta tashi a Bankin Sterling

Ban Ki Mon ya Shugabanci Kungiyar ta Duniya har sau biyu. Ya hau kujerar ne a shekarar 2006, bayan ya karba daga hannun Kofi Annan. Ban Ki Mon. Majalisar Dinkin Duniya dai ta kusa shekaru 200 da kafuwa a Duniya.

Sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar, Jose Gutierez ya nada wasu mata guda 2 cikin Majalisar. Antonio Gutirres wanda ya zama Shugaban Majalisar na 9 a Tarihi, ya kuma nada Amina J. Mohammed ta Najeriya a matsayin Mataimakiyar sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel