Wasu abubuwa 9 mai ban tsoro da gwamnatin Buhari a shekara 2017

Wasu abubuwa 9 mai ban tsoro da gwamnatin Buhari a shekara 2017

To dai ‘yan Najeriya sun nuna fargaba ga gwamnati Buhari a shekara 2017.

Yayinda muka yi bankwana da shekarar 2016, a wanna shekara de ‘yan Najeriya sun fuskanci masaloli daban-daban a hayuka na yau da kulum, daga koma bayan tattalin arziki da fadiwan farashin mai a kasuwan duniya.

Shugaban kasa muhammadu Buhari tare da jam'iyyar APC ta yi wa ‘yan kasa alkawari canji. Sun yi wa jama’a wa’adi habubuwa da dama a lokacin yaƙin neman zaɓe. Ama kuma a yanzu dai babu wata alama canji a jikin mutane Najeriya.

Ko da yake wasu sun cire zamani a cikin wannan gwamnati, wasu kuma har yanzu suna fatan da cewa abubuwa mafi alhẽri za su samu.

Wata Sabuwar Shekara ta fara yanzu. Shin, me nene manufar gwamnati ga ‘yan Najeriya, alheri ko sharri a shekara ta 2017? Wasu daga cikin rahayi ‘yan Najeriya:

1. Tsaro

Sheakara da ta gabata ne rundunar sojin kasa ta durkushe duka sansanin ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa ta arewa maso gabas a ya yin da ta kawo karshen Boko Haram.

Duniya gaba daya ta yaba shugaba Buhari da kuma gwanintan rundunar sojin Najeriya da cin nassara. Duk da haka, gwamnati har yanzu yana da sauran matsalolin tsaro a yanki daban-daban kamar Fulani makiyaya, ‘yan bindiga Neja Delta, tsẽgumi Biafra da ‘yan Shi'a.

Ya kamata gwamnati ta magance wadannan matsaloli kai tsaye a cikin shekara 2017.

2. Rashin aikin yi ga matashi

A shekara da ta gabata da yawa 'yan Najeriya sun rasa ayyukan yi, rahoto daga ofishin lissafi ta kasa yayi karin bayanin cewa a kala mutane 1.7 miliyan ne suka rasa ayyukan yi a shekara 2016.

Shin shugaba Buhari sai samar da sabobin ayyuka 1 miliyan a kowani shekara yan da ya wa ‘yan Najeriya alkawari?

3. Durkushewar tattalin arziki

A wata Agusta da ta gabata Najeriya ta shiga wa ta salo koma bayan tattalin arziki.

Kafin nan, daraja naira ta fadi kuma har yanzu ta na kan fadiwa a bisa ga kudin kasashen woje.

Durkushewar tattalin arzikin na bukatan canji. Talakawa na bukata canji ta hanyoyi manufofin gwamnati tarayya. Wanna ne kawai sai ‘iya kawo wa kasa cigaba da a ke bukata.

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa, kasafin kudin ta 2017 da ta shifanta da kasafin kuɗi na farfadowar da kuma ci gaban tattalin arziki sai kawo wasu gyara a nan gaba kadan.

‘Yan Najeriya dai na jira da fatan cewa za a farfado da tattalin arzikin a wannan shekara ta 2017.

4. Cin hanci da rashawa

Gwamnati tarayya na iya kokarin cewa ta kawo karshen ci hanci da rashawa a fadin kasan nan. A cikin kokarin ta Hukumar kula da Laifukan kudi da kuma Tattalin arziki ya kama wasu shahararren 'yan Najeriya fiye da 30 wa yanda zu ka yi awon gaba da dukiyoyin al’umma.

A yanzu dai ‘yan Najeriya na jigaba da furta albarkacin bakin su, shin mai ya sa gwamnati ta gagara bayyana sunayyen wayanan kwararu barawon gwamnati.

5. Kokarin murkushe ‘yan adawa

Many have expressed concerns that the ruling APC was hiding under the cloak of fighting corruption to cripple the opposition ahead of 2019 general elections. Some have accused the ruling party of trying to turn the country into a one party state.

Mutane da yawa sun bayyana damuwa zu cewa mulkin jam’iyyar APC ta boye a karkashin inuwar yaki da cin hanci don ta murkushe’yan adawa kafin zaben kasa mai zuwa a shekara 2019. Wasu sun zargi jam'iyyar na kokarin mai da kasar a cikin wata ƙungiya daya.

6. Yawan zargi

Tun da APC ta karbi mulki daga jam’iyyar PDP, har yanzu ba ta dena yawan zargi da ta ke ma jam'iyyar ba, durkushewar tattalin arziki, rashin wutar lantarki, rashin aikin yi da saura habubuwa daban-daban. ‘Yan Najeriya sun gaji da wadannan batutuwa gwamnatin Buhari. Mutane sun yi lahakari cewa in de wannan zargi ta cigaba a haka, gaskiya ba za cinma wa ta manufa ba.

7. Ba wani takamaiman canji

‘Yan Najeriya sun yi tsammanin alheri a lõkacin da shugaba Buhari ya hau kan mulki da cewa sun yi zaton shi ne Almasihu da zai cece su daga mulkin jam’iyyar PDP . Ama Abubuwa sun yi muni bisa ga yadda a ka saba abaya.

Gwamnatin ya gama shirin saya wasu motoci guda bakwai ga tsohon shugabannin kasa da kuma mataimakin su da kudi kimani miliyan 400 a inda wasu jihohi na famar da rashin biya albashi ga ma’aikata.

8. Yin alkawari ba tare da wata mataki

Yayinda mutane da yawa na jira alkawuran da aka yi da wannan gwamnati wadda har yanzu ba a cika ba. 'Yan Nijeriya sun gaji da alkawuran. Suna so su gani a kasa. Tsoron shi ne cewa gwamnati za ta cigaba da yin alkawuran da ba zai iya cika ba.

9. Ministocin sun kasa burge 'yan Najeriya

Sai da ya dauki gwamnatin Shugaba Buhari wattani shida kafin ya bayyana wa jama’a ministocin za. A yanzu ayukan su ba ta burge 'yan Najeriya ba, wasu sun bukaci shugaban Buhari ya canza wasu.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa da https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel