Gwamnati ta fara biyan mutane miliyan daya masu karamin karfi N5000 duk wata

Gwamnati ta fara biyan mutane miliyan daya masu karamin karfi N5000 duk wata

Gwamnatin tarayya karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fara cika alkawarin data dauka na biyan naira 5000 ga marasa karfi a Najeriya don rage radadin talauci.

A karkashin shirin bada tallafin, gwamnati zata dinga biyan talakawa yan Najeriya su miliyan daya N5000 a kowane wata don rage musu radadin tsananin halin rayuwa. Jaridar Tribune ta ruwaito gwamnatin tarayya tana sanar da fara biyan wadannan kudade.

Gwamnati ta fara biyan mutane miliyan daya masu karamin karfi N5000 duk wata

Kaakakin mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ne ya bayyana haka, inda yace wannan na daga ciki manufofin gwamnatin shugaba Buhari na taba rayuwan yan Najeriya.

KU KARANTA: Buhari ya tumɓuke Babachir daga shugabantar kwamitin tsara sabbin hukumomin gwamnati

Buhari ya tumɓuke Babachir daga shugabantar kwamitin tsara sabbin hukumomin gwamnati

“An saki kashin farko na kudaden tallafa ma yan Najeriya talaka su miliyan daya na garuruwa hudu a satin daya gabata zuwa bankin tsarin sasanta bakuna (NIBSS) wanda itace bankin dake da hakkin kula da kudaden baiwa jama’a tallafi. Za’a saki na garuruwa biyar nan bada dadewa ba,” inji shi.

Laolu ya kara da cewa a yanzu haka an fara biyan kudaden a garuruwan Bauchi, Kwara, Borno, Kros Riba, Neja, Kogi, Oyo da jihar Ekiti. An fara daga jihohin tara da aka lissafo ne saboda sune masu cikakken rajistan marasa talakawa marasa karfi, sa’annan kuma a baya anyi kokarin kamanta irin wannan tsarin a jihohin tare da hadin gwiwar bankin Duniya.

“Sa’annan karin jihar Borno da aka gani, anyi shi ne sakamakon akwai sahihin rajistan yan gudun hijira a jihar, kuma ana sa ran za’a cigaba da gudanar da tsarin a kafatanin jihohin kasar nan.

“Sakamakon hadin gwiwa da bankin duniya, ana shirin amfani da tsarin bankin duniyan don tattara rajistan talakawa masu karamin karfi a dukkanin jihohin don tantance wadanda yafi dacewa su amfana da shirin bada tallafin,” inji Laolu.

Sanarwar ta kara da cewa bankin NIBSS ce zata dinga gudanar da aikin biyan kudaden da zarar an tabbatar da masu amfana. A wani labarin kuma gwamnatin tarayya ta fara biyan N30,000 ga matasa 200,000 da ta dauka aikin koyarwa, aisibiti da malaman gona a karkashin tsarin N-Power.

Kamfanin dillancin labarai ce ta mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkar watsa labarai Laolu Akande yana bayyana haka a ranar 30 ga watan Disamba inda yace “duk wadanda aka tantance a tsarin N-power zasu dinga amsan kudadensu ta asusun bankin da suka bayar.” Laolu yace kashi na farko sun amshi kudinsu a ranar 30 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel