Fastocin Najeriya na jabu ne, an maida martani ga wahayin da akayi game da Buhari

Fastocin Najeriya na jabu ne, an maida martani ga wahayin da akayi game da Buhari

- Yan Najeriya sun kai hari ga wani babban malamin coci da yayi hasashen mutuwar shugaban kasa Buhari kan kafofin zumunta saboda wahayinsa

- Yan Najeriyan da suka yi sharhi a kai sunyi amfani da daman gurin nuna fushin su a kan fastoci sun kira su gaba daya a matsayin makaryata kuma mazambata

- Sun bukaci sauran yan Najeriya da karda su yarda fastoci su dunga yaudarar su da kalamansu

Fastocin Najeriya na jabu ne, an maida martani ga wahayin da akayi game da Buhari
Fastocin Najeriya na jabu ne, an maida martani ga wahayin da akayi game da Buhari

Yan Najeriya sun maida martani ga has ashen mutuwa ga wani fasto mazaunin Asaba wanda yayi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mutu kafin karshen 2019.

A wahayin san a sabon shekara, Prophet Emmanuel Chukwudi na cocin Kings Deliverance Church, yayi has ashen mutuwar shugaban kasa kafin shekarar 2019 ya kare.

KU KARANTA KUMA: Najeriya za ta kasance mafi muni, idan ba don Buhari ba– Okumagba

Manzon ya fuskanci kalu bale da dama a kafofin zumunta kuma yay an Najeriya da dama sun fito don harin manzon, sun bayyana a matsayin manzo na jabu.

Saboda haka, yan Najeriya sunyi amfani da daman gurin hari ga sauran manzannin da fastocin, sun bayyana su a matsayin na jabu kuma mazambata kan wahayinsu.

Mohammed Muktar Musa, wani mai amfani da shafin Facebook, a sharhinsa yace: “Ina mamakin yadda wasu mutane basu da hankali sai su dunga sauraron karya daga mutanen dake kiran kansu a matsayin manzanni. Babu shakka a kasar Najeriya kawai ne muke da irin wadannan mahaukatan, marasa hankali kuma jahilai da suke da ra’ayin sauraron irin wannan karyan. Abun kaico ne cewan wasu wawaye sun yarda da irin wannan karyan.”

Wani mai amfani da shafin, Emma Itodo Abu, a bangarensa ya bayyana cewa. “Ba mazanni bane, alamu ne na karshen zamani, saboda yesu a cikin injila yace a ranar karshe, mazannin karya da dama zasuyi amfani da sunana, cewa ni wannan ne, amma kuyi addu’a sosai saboda karda ku fada a tarkon su.”

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali a Ilorin kan rikicin addini

Onaiwu Kelly Erhabor yace: “Dukka wahayin shirme, a karshen shekarar 2015 dukkansu sunyi has ashen cewa wani tsohon shugaban kasar Najeriya zai mutu,amma babu wanda ya mutu duk da cewan mun sa rai ga haka saboda yadda suka halaka kasar.”

Yusuff Quadriya bukaci yan Najeriya da karda su yarda a yaudare su: “ku dakatar da abunda kuke yi kuyi aiki da hankulan ku… idan dukkan wahayin nan daga bayin Allan nan gaskiya ne daga Allah, mai yasa bai zama day aba…SMH… wasu lokutan nakanyi mamakin dalilin da yasa ba’a hukunta su…Ta yaya zaka bude bakin ka kayi ma wani has ashen mutuwa?”

Asali: Legit.ng

Online view pixel