Ghali Na’Abba ya kafa wata sabuwar kungiyar siyasa

Ghali Na’Abba ya kafa wata sabuwar kungiyar siyasa

- Tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na'abba ya jagoranci wata sabuwar kungiyar siyasa a Kano.

- Na’Abba ya ce, sun kafa kungiyar ne domin ceto siyasa da kuma ‘yan siyasar kasar daga bakin kura

Ghali Na’Abba ya kafa wata sabuwar kungiyar siyasa
Ghali Na’Abba ya kafa wata sabuwar kungiyar siyasa

Alhaji Ghali Umar Na'abba, tsohon kakakin majalisar wakilai ya zama shugaban sabuwar wata kungiyar siyasa a Kano mai suna 'Siyasar Kano ina Mafita', Daily Trust ta rawaito.

Tsohon kakakin, yayin da ya ke kaddamar da kungiyar ya ce kafa kungiyar ya zama dole, ganin yadda jam'iyyun siyasa ke danne wa 'yan siyasa hakkokinsu a jihar.

Na'abba ya kuma ce babban dalilin kafa kungiyar shi ne don nemo mafita ga wadanda a ke dannewa.

Ya ce, "Mun ga barnar da a ka yi wa dimokaradiyya a Najeriya kimanin Shekarau 20 yanzu. Kuma za ku yarda da ni sakamakon da waccan barnar ta haifarwa siyasar Najeriya ya fada kan siyasa ne".

"Mun tambayi kan mu har yaushe za mu ci gaba da nade hannun mu muna ganin al'amura su na dada lalacewa. Lokaci ya yi da za mu hada kai mu nemo hanyar da za mu 'yanta siyasa da 'yan siyasar Najeriya."

Daya daga cikin dattijan kungiyar, Farfesa Sule Bello ya ce, ko a wace jam'iyya ka ke za ka iya shiga kungiyar don 'yanta dukkan 'yan siyasa da a ke dannewa.

A Kano, 'ya'yan jam'iyyar APC su na danganta kansu ne da ko dai Kwankwasiyya, ta magoya bayan tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso, ko kuma Gandujiyya, ta magoya bayan gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Abin da ba a sani ba shi ne ko kungiyar ta kawo mafita ne ga wadanda a ka batawa a daya daga cikin wadancan gidaje.

Na'abba wanda tsohon dan jam'iyyar PDP ne ya wakilci karamar hukumar Birni da Kewaye a majalisar wakilai ta kasa daga 1999 zuwa 2003.

A watan Agusta na 2009, ya na daya daga cikin tsaffi da shuwagabanni masu ci da su ka kafa Gamayyar' 'Yan Siyasa don Kawo canji a yanayin zabe a kokarin su na kawo canji a kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

Asali: Legit.ng

Online view pixel