MMM tace zata bude asusun kudin jama’ a 14 ga Junairu

MMM tace zata bude asusun kudin jama’ a 14 ga Junairu

MMM Nigeria ta bayyana cewa za’ a bude asusun a ranan 14 ga watan Junairu, 2017

Kosawa na masu hannun jari a asusun ajiyar kudin ruwa Mavrodi Mundial Movement, (MMM) zata cigaba yayinda masu kula da asusun sun ce zasu bude asusun mutanen da ta daskarar.

MMM Nigeria ta bayyana cewa za’ a bude asusun a ranan 14 ga watan Junairu,2017.

Zaku tuna cewa a ranan talata,13 ga watan Disamba 2016, MMM ta daskarar da asusun masu hannun jari a asusun ta hana su cire kudinsu na tsawon wata daya.

Masu hannun jari sunyi tunanin ranan 13 ga junairu ne za’a bude asusun,amma MMM ta bayyana ta asusunta na shafin Tuwita cewa zasu bude asusun mambobinta a ranan 14 ga watan Junairu 2017.

KU KARANTA: Dan takara ya tona asirin gwamnoni

Suka ce: “Munyi alkawari da mambobinmu cewa za’a bude asusun mutane( watau zasu iya cire kudi) daga 14 ga watan Junairu 2017. Saura kwana 12.”

A bangare guda, wasu yan Najeriya sun tuhumci gwamnatin tarayya da sanya hannun jari cikin MMM,sakamakon rahotannin karancin kananan kudi a fadin kasa.

Wannan tuhuma na zuwa ne bayan wasu majiya a bankin CBN sun bayyana cewa bankin ba zata iya buda kananan kudi ba saboda matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel