Yan sandan Uganda sun rushe auran yar shekara 14 (hotuna)

Yan sandan Uganda sun rushe auran yar shekara 14 (hotuna)

Yan sandan sun rushe wani bikin aure tsakanin yar shekara 14 da mutun dan shekara 22.

Daily Monitor ta ruwaito cewa yarinyar wacce ta bar makarantar Sakandari, tana da cikin watanni hudu a yanzu.An ce Iyayenta, Abdu Kalimu Ngobi da Faridah Kagoya sun yarda su aurar da yar tasu ga mutumin, Talyaka Swaliki bayan sun karbi Shs 200,000 da kuma akuya a matsayin sadaki.

Yan sanda sun iso gurin bayan an kammala auran gargajiyan sannan kuma a lokacin mijin na shirin tafiya da amaryarsa gida. Dukkan bakin da suka halarci bikin da yan uwansu suka gudu don karda a kama su.

Yan sandan Uganda sun rushe auran yar shekara 14 (hotuna)
Kamramar amaryan da ake magana a kanta

Ga mamaki, amaryar ta karyata cewan shekarunta 25 inda ta kuma yi ikirarin cewa shekararta 28. Tace ” Ni ba yarinya bace kuma ban san dalilin da yasa yan sanda suka tarwatsa auranmu ba. Ina son mijina. Na nemi izinin iyayena kafin nayi aure.”

KU KARANTA KUMA: Buhari zaiyi shekaru 8 a kan kujerar mulki – Soul E ya saki wahayin 2017

Haka kuma iyayen yarinyar sun nace kan cewa shekarun yarsu 18 kuma sun yarda sun aurar da itane kamar yadda ta bukata. “ Ta bar makaranta kuma ta fada mana cewan tana son ta auri mutumin da yayi mata ciki kuma a matsayin musumi, bani da zabi,” cewar mahaifinta, Mr Ngobi.

Yan sandan Uganda sun rushe auran yar shekara 14 (hotuna)
Uban amaryan (hagu) angon (dama)

Angon ma yace ya kasance yana soyayya da yarinyar tsawon shekaru biyu.

“Iyayenta sun bukaci sadakin Shs 200,000, akuya da gomesi biyu wanda kuma na biya. Basu fada mun cewa yarinya bace,” cewar angon.

Ko da yake wasu kungiya nay an unguwar daga baya sun isa ofishin yan sandan inda suka bukaci a saki mai laifin, yan sandan sun tabbatar da cewa za’a caji iyayen kan aurar da yarinya karama yayinda za’a caji mijin da laifin aikata kazanta.

Allah ya kyauta!

Asali: Legit.ng

Online view pixel