Abin kunya hukumar DSS da guntsawa Sahara Reporters hirarrakin'yan Najeriya a wayar tarho

Abin kunya hukumar DSS da guntsawa Sahara Reporters hirarrakin'yan Najeriya a wayar tarho

Mista Ayodele Fayose ya zargi hukumar tsaro ta farin kaya DSS da nadar hirarrakin tarho na 'yan Najeriyan da a ka ce su na sukar gwamnatin APC ta shugaba Muhammadu Buhari, su tace hirar su kuma guntsawa jaridar Sahara Reporters wanda ya zama wani babban dandali na yada farfagandar gwamnatin tarayya.

Abin kunya hukumar DSS da guntsawa Sahara Reporters hirarrakin'yan Najeriya a wayar tarho
Abin kunya hukumar DSS da guntsawa Sahara Reporters hirarrakin'yan Najeriya a wayar tarho

Fayose ya bayyana nadar hirarrakin wayar tarhon 'yan Najeriya da hukumar DSS ke yi ta na guntsawa Sahara Reporters da rashin gaskiya a siyasa da yaudara da danniya da sauransu.

Fayose ya bayyana abin da DSS ke yi a matsayin abin kunya.

Gwamna Fayose ya ce shi bai damu ba da abin kunyar na gwamnatin tarayya, ya kara da cewa: "Maimakon zama a na sa ido ga wayoyin mutane, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta samar wa 'yan Najeriya abinci sannan ta ceto rayukan wadanda a ke kashewa a Kudancin Kaduna."

Gwamnan wanda ke mayar da martani kan hirarsa da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da Sahara Reporters su ka wallafa, ta hanyar mataimakinsa kan sadarwa da kafofin sadarwa na zamani, Lere Olayinka ya ce:

"Idan shugaban kasa da 'yan barandarsa a DSS da EFCC da wasu hukmomin gwamantin tarayya ba su san mai ya kamata su yi ba, sai nadar hirarrakin wayar tarho na wadanda su ke wa kallon 'yan adawa, to gara su ajiye aikinsu don ceto Najeriya daga wannan mummunan yanayi."

Gwamnan ya bayyana nadar hirarrakin wayar tarhon 'yan Najeriya da DSS ke yi suna guntsawa Sahara Reporters a matsayin rashin gaskiyar siyasa da yaudara da danniya da sauransu. Jami'an gwamnatin tarayya na ta kokarin rufe laifuffukan da su ka yi wa jama'ar jihar Rivers.

"Kamata ya yi su wuce nadar wayoyin tarho su zo su zauna da ni a gidan gwamnatin Ekiti ko sa dinga nadar duk abinda na ke fada duk dakika daya, saboda a shekarar 2017 da yardar Ubangiji zan fadi wasu maganganun ba tare da nadama ba."

Gwamna Fayose ya ce a karo na farko tun bayan dawowar mulkin dimokaradiyya a shekarar 1999, 'yan Najeriya su na bukukuwan Kirsimeti cikin yunwa da wahalhalu fiye da kima.

"Yan Najeriya na bukatar abinci, su na bukatar aikin yi, su na bukatar tsaro, ba nadar hirarrakin wayar tarho da mika wa dandalin yanar gizon kan hanya ba.

"Rashin aikin yi na karuwa sosai yayin da tsarin zabe ke kara lalace wa.

"Maimakon su magance matsalar yunwa da matsalolin tattalin arzikin kasa, sun buge da dabarun kawar da tunanin mutane da maganar hirar wayar tarhon gwamna Wike da gwamna Fayose, gwamnonin da ba su da sojoji kuma ba su da iko da tsaron kasa." A cewar gwamnan.

Ya ce:

"Na sani ba tun yau ba cewa a na sa ido a kan hirarrakin wayar tarhon fitattun 'yan Najeriya, musamman 'yan majalisa da 'yan adawa, amma ba na damuwa na sauke nauyina na ceto Najeriya daga mulkin danniya wanda gwamnatin APC ke yi a yanzu."

Yayin da ya yadda cewa gwamnatin tarayya ta APC ba ta girmama dokokin kasa. A fadar gwamna Fayose.

Sun sani cewa abinda su ke yi ba ya kan doron doka kuma ya sabawa sashi na 37 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 wanda ya ce:

'Sirrin 'yan kasa da wasikunsu da hirarrakin wayar tarho da sadarwa ta telegraph dole ne a basu kariya.'

"To amma saboda su makirai ne kuma su na gudanar da mulkin kama karya ta hanyar amfani da DSS da EFCC da wasu hukukomin, mutum ba zai mamakin abin da ke faruwa a yanzu ba."

Ya nemi 'yan Najeriya da kada su zuba ido ga wannan kama karyar, ya na mai cewa; 'wata rana sai ta zo kan kowa."

Ya ce

"Kamar yadda na fada a baya, tsarinsu ya zama ruwan dare. Duk lokacin da 'yan Najeriya su ka koka game da wahalar da su ke sha, sai su fara kawo soki burutsu." "An samu biliyan 1 a dakin wane ko wane ko wance.

"An murkushe Boko Haram. Mun kama dajin Sambisa. Hirar wayar tarho tsakanin Fayose da Wike ta fita.

"Abin takaici gwamna Wike da Fayose da ba su da karfin soja sun zama babban cikas dinsu yayin da jami'an su da ke da makamai kuma su ke amfani da su a kan 'ya Najeriya ba a tuhumar su.

"La'akari da radadin da ' yan Najeriya ke sha saboda rashin iya aikinsa, idan zan ba shi shawara ba boye-boye, zan ce masa ya sauka saboda ya kunyata ' yan Najeriya da ya yaudare su ya samu kuri'arsu. A mulkinsa yanzu dala 1 naira 500 ce, ga matsananciyar yunwa a kasa, ga shi a na kashe 'yan Najeriya a Kudancin Kaduna da wasu guraren. Ya fi kyau shugaban kasa ya ajiye aikinsa tunda ta bayyana ba zai iya ba. In da duk shugabannin da su ka yi mulki kafin Buhari sun yi irin abinda ya ke yi a yau to da shi kansa yanzu ya garkame a gidan yari.

"Bara na kara fada, ni mutum ne da ba ya tsoron mutuwa ko shiga gidan yari. Zan ci gaba da fadawa 'yan Najeriya gaskiya wadda ita ke batawa Buhari da fulogansa rai.''

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel