Wani Malami ya dubo lokacin da Shugaba Buhari zai mutu

Wani Malami ya dubo lokacin da Shugaba Buhari zai mutu

– Wani Malamin Addinin Kirista yace Shugaba Buhari ya kusa mutuwa

– Sannan Faston yace Kasar Biyafara za ta balle

– Wannan dai yana cikin duban da ya gano

Wani Malami ya dubo lokacin da Shugaba Buhari zai mutu
Wani Malami ya dubo lokacin da Shugaba Buhari zai mutu

Wani Fasto a Najeriya ya buga-ya gano cewa Shugaba Buhari ba zai karasa mulkin Kasar nan ba. Malamin Addinin Kiristan ya bayyana cewa ya leko cewa Shugaba Buhari zai rasu ne a cikin shekarar 2019 inda rashin lafiya za ta ci sa.

Faston yace Farfesa Osinbajo, mataimakin shugaban kasar ne zai karbi mulki, kuma zai fuskanci kalubale wajen jagorantar Kasar daga hannun Soji. Wannan dai harsashen wani Fasto ne mai suna Emmanuel Chukwudi da ke garin Asaba.

KU KARANTA: Buhari zai yi shekaru 8 a kan kujera

Babban Faston da ke Jihar Delta ya bayyana irin abubuwan da ya hango cewa za su wakana a shekarar nan. Yake karawa da cewa za a saki Nnamdi Kanu daga Kotu, kuma har a cin ma samun Kasar Biyafara.

Malamin yace an nuna masa cewa dai Najeriya za ta fita daga matsalar tattalin arziki a bana. Mafi yawan Fastoci dai su kan yi nasu harsashen daga abin da suka gano. Sai dai mafi yawancin duk tamkar kanzon-kurege ne, don akasarin hakan ba su faruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel