Jam'iyyar APC ta ce ba ta dantakara shafaffe da mai a zaben gwamnan Anambra

Jam'iyyar APC ta ce ba ta dantakara shafaffe da mai a zaben gwamnan Anambra

- Yanayin siyasar jihar Anambra ya dau zafi yayin da a ke shirye-shiryen zaben gwamna

- Fiye da 'yan takara goma ne kawo yanzu su ka nuna sha'awarsu na jama’iyyar ta tsai da su cike har da gwamna mai ci

Jam'iyyar APC ta ce ba ta dantakara shafaffe da mai a zaben gwamnan Anambra
ko gwamna Willie Obiano zai yi tazarce bayanda APC ta ce ba ta tsayayye?

A wannan shekarar ne dai gwamna Willie Obiano zai kammala wa'adin mulkinsa na farko kuma rahoton cewa zai sake tsayawa takara sa'ilin da jam'iyyar APC ke fuskantar kalubalen wa za ta dauka ya yi mata takara.

Za a gudanar da zabe a Anambra a wannan shekarar ta 2017 kuma a na sa ran gwamna Willie Obiano zai sake tsayawa takara.

Daga cikn 'yan takarar da su ke so jam'iyyar APC ta tsayar da su akwai Chief Obinna Uzor da Cif Johnbosco Onunkwo, da Mista Tony Nwoye, da mista Donatus Okonkwo, da Chief George Muoghalu, da kuma Patrick Ifeanyi Uba.

Amma jam'iyyar ta ce, ba ta da wani dan takara shafaffe da mai a zaben mai zuwa a watan Nuwamba 2017.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Mista Emeka Ibe ya sanar cewa, babu wani dan takarar da suke ke goyon baya. Yayin da ya ke magana a Awka babban birnin jihar.

"Yawan mutanen da su ke shigowa jam'iyyar a yau alama ce da ke nuna cewa APC ce za ta lashe zaben gwamnan Anambra a 2017.

"Mu na da tarihin gaskiya da daidaito a jam'iyyar APC."

Da zarar ka shiga jam'iyyar yau to daidai ka ke da wanda a ka kafa maja da shi.

"Kawai mutanen da ba ma so, su ne wadanda za su kawo matsala. Mu na bukatar mutanen da za su taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a yakin da ya ke da cin hanci da rashawa." A cewar shugaban, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Ibe ya ce, fiye da 'yan takara goma ne kawo yanzu su ka nuna sha'awarsu. Ya ce:

"Muna tattaunawa da 'yan majalisu na jiha, da na tarayya, da kwamishinoni masu ci da suka nuna sha'awar shiga jam'iyyar.

"Wannan ya nuna cewa APC ce jam'iyya ta farko da za ta dare kujerar mulkin garinnan a shekarar 2017."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel