Ban taba karbar cin hanci -Shugaban Hukumar JAMB

Ban taba karbar cin hanci -Shugaban Hukumar JAMB

– Shugaban Hukumar JAMB ya musanya zargin Kungiyar ASUU

– ASUU tace Farfesan ya karbi cin hanci da rashawa

– Farfesa Oloyede yace bai taba karbar cin hanci ba, amma yana karbar kati

Ban taba karbar cin hanci -Shugaban Hukumar JAMB
Ban taba karbar cin hanci -Shugaban Hukumar JAMB

Shugaban Hukumar Jarrabawar nan ta JAMB ya karyata zargin da Kungiyar Malaman Jami’a watau ASUU tayi na cewa ya saba karbar kudi daga hannun ‘Yan kwangila. Farfesan ya karyata wannan zargi, yace ko sau daya bai taba yin hakan ba.

Farfesa Ishaq Oloyode yace bai taba karbar cin hanci daga hannun kowa ba ko ya tsula kudin kwangila ko ace ma ya karbi wata kyauta hannun wani. Farfesa Oloyode yace dan albashin da yake samu ya wadace sa, asali ma ba sa da dawainiya mai yawa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya nemi a hada kai

Shugaban Hukuamr yace ya kan bi sannu wajen karbar kyauta har hannun abokan sa. Yace ko da yake Shugaban Jami’ar Ilorin bai yi wani abin rashin gaskiya ba. Kungiyar ASUU dai ta zarge sa da wanda ya gaje sa da yin sama da wasu Naira Biliyan 2 na Jami’ar Ilorin.

A kwanakin baya ne dai Hukumar JAMB ta daina saida katin nan da ta saba. Shugaban Hukumar ta JAMB din yace Hukumar ta kashe wannan tsari ne domin akwai badakala a cikin ta.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel