Emmanuella da Mark Angel Comedy sun yi hadin gwiwa da NAIJ.com

Emmanuella da Mark Angel Comedy sun yi hadin gwiwa da NAIJ.com

Emmanuella, yar shekara 6 da ta ke nishadantar da jama’a tare da taimakon marikinta, Denilson Igwe of Mark Angel Comedy, kwanannan ta yarda da hada gwiwa da kamfanin jaridar yanar gizo lamba daya Najeriya, watau Legit.ng.

Emmanuella da Mark Angel Comedy sun yi hadin gwiwa da Legit.ng
Emmanuella da Mark Angel Comedy sun yi hadin gwiwa da Legit.ng

Sun kulla yarjeneniya ta hadin gwiwa tsakaninsu da Legit.ng a cikin watan Disambar shekara 2016.

Hotunan wasan barkwancin yarinyar ya sami karbuwa yayin da aka yada shi a Najeriya, kuma a hankula yana shiga duniya baki daya.

Fatacciyar yarinyar, kwanannan ta fito a wani shirin fim din kasar waje mai suna: ‘Survive and Die, da kuma ‘Crowned the Princess of Comedy wanda gwamnatin kasar Austiraliya ta dauki nauyi.

Legit.ng ta na alfahari da kawowa duniya abin da ya yi fice daga Najeriya, hakan ya sa a wannan shekarar, mu ka kayi hadin gwiwa irinsa na farko da Emmanuella Samuel da Mark Angel Comedy.

Tare da wannan sabon hadin gwiwar da Legit.ng, hakan na nufin dukkanin hotunan bidiyonta za’a rinka dorasu a shafuka kamar haka, shafin Facebook na Naij, wanda ya ke da mabiya akalla mutane miliyan 3 da 300,000, da kuma shafukan yada labarai wato ‘NAIJ.com Breaking news’, da, Legit.ng Gossip, da Legit.ng Weddings da kuma Legit.ng Buzz. Hakan yana nufin a kalla mutane miliyan 6 da100,000 za su rinka ganin ayyukanta!

Haka kuma hadin gwiwar da Legit.ng zai tabbatar da ganin hotunan bidiyon na Emmanuella's da Mark Angel Comedy's da ke a shafin Faceboook an gabatar da su ga mutanen Kenya da kuma Ghana, ta hanyar amfani da shafukan TUKO Kenya da YEN.com.gh a shafukan Facebook pages, wanda hakan zai kara kawowa bidiyon wasu masu kallo a kalla mutane miliyan 2.da 700,000 da ke wajen Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel