MASSOB sun roki Buhari da ya bari yan Biyafara su tafi

MASSOB sun roki Buhari da ya bari yan Biyafara su tafi

- Kungiyar MASSOB sashin Cross River sun roki shugaban Kasa Buhari da ya bari su bar kasar

- Sunyi zargin cewa rayuwa a kasar ya zama mawuyaci

- Sun kuma nace cewa akwai rashin adalci sosai a Najeriya

MASSOB sun roki Buhari da ya bari yan Biyafara su tafi
MASSOB sun roki Buhari da ya bari yan Biyafara su tafi

Mambobin kungiyar Movement for the Actualisation of Sovereign State of Biafra, (MASSOB) sun roki shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da ya kyale Biyafara su bar Najeriya”, jardar Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar MASSOB sashi Cross River ne sukayi wannan rokon kwanan nan.

Sun bukaci shugaban kasa da ya basu yancin kansu.

KU KARANTA KUMA: Karda ka barmu mu mutu a karkashin Buhari – MASSOB ga Donald Trump

A wata sanarwa daga jami’in kula da harkokin jama’a, kwamrade Okon Eyo Effiom, mutanen Biyafara a kasar suna fuskantar wahala don zamansu a Najeriya.

A cewarsa bazasu iya ci gaba da jure ma rashin adalcin Najeriya ba

Kwamrade Effiom ya bayyana cewa a halin da abubuwa ke ciki a kasar, gwamnatin Najeriya bata iya biyan bukatun mutanen ta ba yanda ya dace.

A halin da ake ciki, kungiyar MASSOB ta bukaci shugaban kasar Amurka mai jiran gado da ya taimaki mutanen Biyafara, wadanda ke fuskantar barazana a karkashin gwamnatin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel