Abun da Shekau yace wa Buhari a sabon bidiyon sa (Karanta)

Abun da Shekau yace wa Buhari a sabon bidiyon sa (Karanta)

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a wani faifan bidiyo inda ya ke musanta ikirarin gwamnatin Najeriya na fatattakarsu tare da murkushe su a Dajin Sambisa, sansanin da suke garkuwa da mutane da jagorantar hare hare.

Abun da Shekau yace wa Buhari a sabon bidiyon sa (Karanta)
Abun da Shekau yace wa Buhari a sabon bidiyon sa (Karanta)

“Muna nan lafiya, kuma ba wanda ya kore mu zuwa ko ina” in ji Shakau a cikin sakon bidiyon na tsawon mintina 25 da ya fitar yana magana a harshen Larbaci da Hausa.

Shekau ya ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na yi wa mutane karya, wanda a jajibirin Kirsimeti ya bayyana cewa an murkushe ‘Yan Boko Haram tare da korarsu a Dajin Sambisa.

Shugaban na Boko Haram ya fadi a cikin sakon bidiyon cewa babu wata dabara da za ta iya fallasa inda suke buya sai idan Allah ya yarda.

Shekau dai ya sha fitowa yana karyata ikirarin Sojoji akan samun nasarar Boko Haram.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa

Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel