Rikicin yan kasuwa yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a Enugu

Rikicin yan kasuwa yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a Enugu

An salwantar da rayukan mutane Uku a jihar Enugu yayin da rikici ya kaure a kasuwar Awkunanaw a ranar Alhamis 29 ga watan Disamba, inji rahoton kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN).

Rikicin yan Kasuwa yayi sanidyyar mutuwar mutane biyu a Enugu
Rikicin yan Kasuwa yayi sanidyyar mutuwar mutane biyu a Enugu

Kaakakin rundunar yansandan jihar Abere Amaraizu ya tabbatar da mutuwar mutane biyun, sa’nnan yace rikicin ya faro ne tun a ranar Laraba 28 ga watan Disamba yayin da wani mutum ya caka abokin cacar bakinsa wuka.

KU KARANTA:Abin tausayi: Hatsarin jirgi ya rutsa da Sojojin Najeriya

Hakan ne ya sanya sauran jama’a suka far ma mutumin, inda suma suka yi mai dukan tsiya, inda ya mutu a asibiti.

Ebere yace: “Mun tabbatar da mutuwar mutane 2 a jiya sakamakon rashin jituwa da suka samu a tsakaninsu da yammacin ranar Alhamis a kasuwar Gariki dake Awkunanaw. Mun aika da karin jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya a kasuwar.”

Kaakakin ya karkare da cewa, “a yanzu mun fara bincike don gano musabbabin rikicin.”

NAN ta ruwaito cewar ba’a san takamaimen ummul aba’aisun rikicin ba zuwa yanzu, amma ana tsamman mamatan kodai yan tireda a kasuwan ko kuma yan tasha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel